‘Fiye da rabin kalmomin Hausa sun samo asali ne daga Larabci’

‘Fiye da rabin kalmomin Hausa sun samo asali ne daga Larabci’
An wallafa

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 18 ga watan Disamban kowacce shekara don kasancewa Ranar Harshen Larabci ta Duniya.

Taken ranar na wannan shekara shi ne 'Rawar da Harshen Larabci ke Takawa a Fannin waƙa da Ƙirƙira'.

Larabci dai na ɗaya daga cikin manyan harasa da ke da yawan amfani da shi a duniya

Shugaban hukumar nazarin Larabci da ilimin addinin musulunci ta Najeriya, NBAIS, Farfesa Yahuza Sulaiman Imam ya ce an ware ranar ce domin nuna wa duniya irin rawar da harshen ke takawa wajen ci gaba da bunƙasa da kuma muhimmanci da gudunmowar da harshen ke bayarwa wajen ci gaban duniya.

Farfesa Yahuza ya ce wannan ne karo na 11 ga ake gudanar da irin wannan bikin, tun bayan da hukumar kula al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya Unesco ta ƙirƙaro ranar.

Ya ce Larabci ya taka muhimmaiyar rawa wajen abin da ya shafi rubutun zube da ƙirƙire-ƙirƙire.

Ya kara da cewa harshen Larabci ya shiga cikin wasu harasa da dama inda ya cinye wasu, ya bayar da misali da harshen Swahili, in da ya ce kaso 80 na kalmomin da ake amfani da su a harshen, kalmomin Larabci ne.

Shugaban hukumar ta NBAIS ya kuma ce kusan kashi 60 na kalmomin da ake amfani da su a harshen Hausa, daga harshen Larabci aka aro su.

"Kama daga abin da ya shafi lissafi da ƙidayar kwanaki da harkokin siyasa da kalmomin addini duka daga harshen Larabci aka aro su'', in ji shi.

Sai dai ya ce harshen na fuskantar ƙalubale daga manyan harasa da ke gogayya da shi musaman a Najeriya da sauran ƙasashe.

''Kamar Turanci na goyayyada shi a Najeriya, Faransaci a ƙasashe renon Faransa''.