Ra'ayi Riga: Kan yawan bashin da Najeriya ke karɓowa 23/11/2024

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Kan yawan bashin da Najeriya ke karɓowa 23/11/2024
An wallafa

Tsawon shekaru gwamnatoci a Najeriya sun mayar da hankali wajen karɓo bashi domin gudanar da kasafin kuɗin a kowacce shekara.

Bashi na baya-bayan nan shi ne na naira tiriliyan 1.7 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar ƙasar, kuma ya samu sahalewar majalisar.

Sai dai masana na nuna damuwa kan yawan bashin da gwamnatocin ke ciyowa, lamarin da suke gani babbar barazana ce ga tattalin arzikin ƙasar.

Shin waɗanne hanyoyi ya kamata gwamnatoci su bi wajen samun kuɗaɗe ba tare da dogaro da bashi ba wajen gudanar da kasafin kuɗi?

Batun da shirin na wannan makon ya tattauna kenan.