...Daga Bakin Mai Ita tare da Wasila Isma'il
A wannan makon mun kawo muku tauraruwa Wasila Isma'ila wadda ta fara fitowa a wani fim mai suna Jinin Masosya a 1998.
To sai dai tauraruwar wadda aka haifa kuma ta yi duk rayuwarta a Kaduna, ta fi shahara da sanuwa a wani fim mai suna Wasila.
"Lokacin da fardusa ya faɗa min cewa zan taka rawa a fim ɗin Jamila sai na nemi alfarmar a mayar da sunan fim ɗin zuwa Wasila. Sai fardusan ya nemi jin dalili sai na ce masa saboda ba na son Jamila domin ka da a ɓata min suna. Kuma ya yarda." In ji Wasila.
Dangane da rawar da ta taka a fim ɗin, Wasila ta ce "ban yi da-na-sani ba kuma ban samu wani ƙalubale ba duk da rawar da na taka a fim ɗin. Moɗa ne dai ya fuskanci ƙalubale a wurin masu kallo domin a lokacin jama'a suna ganin kamar fim gaske ne."
Wasila ta ƙara bayani kan dalilin da ya sa aka kwashe dogon lokaci ba a ganin ta.
"Gaskiya na fahimci yadda aka takura min a duk lokacin da na shiga cikin jama'a. A lokacin idan bisa tsautsayi na fita unguwa, wani lokacin sai an zo da ƴan sanda kafin a fitar da ni.
Hakan ne ya sa wata rana na birkicewa ƴan gidanmu cewa ni kawai aure nake so. Kuma na samu haɗin kai aka yi min aure na huta. Kuma na zauna da maigidana lafiya har ma na haifi ƴaƴa biyar" In ji Wasila.
To sai dai kuma daga baya Wasila ta ce "dole ce ta saka na sake dawowa harkar fim saboda yanayin buƙatar da iyalaina suke kama daga karatunsu, abincinsu da tufafinsu."



