Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli yadda gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Fanteka ta Kaduna
Kalli yadda gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Fanteka ta Kaduna
An wallafa
Wata gobara da ta tashi a ƴan katako a tsohuwar kasuwar Fanteka da ke jihar Kaduna, Najeriya, ta yi sanadin ƙonewar rumfuna aƙalla 250 da salwantar dukiya mai ɗumbin yawa.
Shugaban kasuwar, Alhaji Sulaiman Shehu ya shaida wa BBC cewa ibtila'in da ya faru a daren Laraba, ya shafi wani ɓangaren ƴan katako ne a cikin tsohuwar kasuwar ta Fanteka.