'Faston da ya sanya mabiyansa yin azumin mutuwa mutumin kirki ne'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
'Faston da ya sanya mabiyansa yin azumin mutuwa mutumin kirki ne'
An wallafa

Yayin da ake ci gaba da gano gawarwakin mutane waɗanda ake zargin sun mutu sanadiyyar azumin da suka yi na haɗuwa da Yesu a Kenya, wani ɗan uwan faston da ke jagorantar ƙungiyar ya tattauna da BBC.

Robert Mbatha ya ce a iyakar sanin sa fasto Paul Nthenge mutumin kirki ne, sai dai bai sani ba ko halinsa ya sauya daga baya.

Fasto Paul Nthenge
Bayanan hoto, Fasto Paul Nthenge