Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Burina gina al’ummar jihar Kano idan na zama gwamna'
'Burina gina al’ummar jihar Kano idan na zama gwamna'
An wallafa
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar SDP, Bala Muhammad Gwagwarwa ya ce zai fi bai wa ‘gina al’umma’ muhimmanci idan har ya samu nasarar zama gwamnan Kano.
Dan takarar wanda ya zayyana wasu manufofi da ya ce zai mayar da hankali a kansu.
Ya kuma yi kira mutanen jihar ta Kano da su kula ka da su yarda ‘a saye su da kudi saboda kudinsu ne da ya kamata a yi musu ayyukan raya kasa da su.’