Ingila ta gayyaci matashin Man City Lewis a karon farko

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta mika goron gayyata a karon farko ga matashin dan wasan Manchester City, Rico Lewis.

Kenan yana cikin 'yan kwallon Ingila da za su buga karawar neman shiga gasar Euro 2024 da kasar za ta kece raini da Malta ranar Juma'a da kuma North Macedonia ranar Litinin.

Mai shekara 18, wanda ya fara ciki daga makarantar koyon tamaula, ya buga wasa 10 kawo yanzu a bana.

Ya taka rawar gani a bara a kakar da City ta lashe Champions League da Premier League da kuma FA Cup.

Dan wasan wanda ke buga tsakiya tun farko yana cikin matasan Ingila 'yan shekara 21 da ya kamata su kara da Serbia ranar Talata da kuma Ireland ta Arewaa wasan neman shiga gasar matasa ta Euro 2025

To sai yanzu Lewis, wanda ya buga wa matasan Ingila karawa hudu, zai koma yiwa babbar tawagar Inglila wasanni.