Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Premier za ta ci karo da tsaiko sakamakon gasar Afirka da ta Asiya?
Wasu kungiyoyin Premier League za su rasa 'yan wasa da za su buga wa kasashensu gasar kofin nahiyar Afirka da masu buga Asian Cup a Janairun nan.
Za a fara gasar Asian Cup a Qatar tsakanin 12 ga watan Janairu zuwa 13 ga watan Fabrairu.
Za a fara gasar Kofin Afirka a Ivory Coast daga 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu.
'Yan wasa da yawa ba za su samu damar buga Premier League da FA Cup da kuma Carabao Cup a lokacin ba.
Mohamed Salah, Liverpool
Bincike ya nuna yadda magoya bayan Liverpool ke nuna damuwa kan rashin Mohamed Salah da zai je buga wa Masar gasar cin Kofin Afirka.
Salah ya taimaka wa Liverpool wajen cin kwallo 22, ya zura 14 daga ciki, ya bayar da takwas aka zura a raga.
Haka kuma ya ci kwallo na 150 a Premier League a wasan da Liverpool ta doke Newcastle United.
Salah ba zai buga wa Liverpool karawar daf da karshe ba a Carabao, ga kuma karawar FA Cup nan gaba.
Haka kuma Liverpool za ta yi wasanni ba tare da dan kasar Japan Wataru Endo ba, wanda zai je Asian Cup.
Tottenham za ta yi rashin Son
Tottenham na sa ran lashe Premier League a bana, wadda take fama da ƴan wasan da ke jinya, sannan kyaftin dinta Son Heung-min zai je buga Asian Cup tare da tawagar Koriya ta Kudu.
Tottenham tana ta biyar a Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Arsenal ta hudu, da Manchester City ta uku, da tazarar maki shida tsakaninta da Liverpool ta saman teburi.
Son na taka rawar gani a Tottenham, wanda ya ci kwallo 12 a Premier League. Wadanda ke gabansa sun hada da Mohamed Salah da kuma Eerling Haaland.
Haka kuma Tottenham za ta yi rashin 'yan wasan da za su je buga gasar Kofin Afirka da suka hada da Pape Sarr da kuma Yves Bissouma.
Wasu Ƴan wasan Premier League da za su buga ko dai Afcon ko kuma Asia Cup
Bayan Liverpool da Tottenham da za su rasa ƴan wasa, Manchester United za ta ci gaba da wasanni ba tare da mai tsaron ragar Kamaru ba, Andre Onana, da ake sa ran dan Turkiya, Altay Bayindir zai maye gurbinsa.
Wolves za ta ci gaba da fafatawa ba tare da Hwang Hee-chan na Koriya ta Kudu ba, wanda ya ci mata kwallo 10.
Yayin da Antoine Semenyo (Bournemouth), Yoane Wissa (Brentford) da Nicolas Jackson (Chelsea) da Jordan Ayew (Crystal Palace) da Alex Iwobi (Fulham) da Mohammed Kudus (West Ham) za su je buga gasar cin Kofin Afirka a Ivory Coast.
Ƴan wasan Nottingham Forest kusan shida ne za ta rasa a dan lokacin nan.
Burnley
Dan kwallon Afirka ta Kudu, Lyle Foster, ba zai je Afcon ba, Ya gana da kwararren likita kan ciwon damuwa, wanda bai yi wasa ba mako takwas, amma ya koma fagen daga a watan jiya.
Kociyan Burnley Vincent Komfani ya ce Foster bai shirya buga Afcon ba, amma zai iya buga wa Burnley wasanni.
Mai shekara 23 ya ci kwallon farko bayan da ya koma taka leda a karawa da Aston Villa ranar Asabar.
Manchester City da Newcastle ba za su rasa ƴan wasa ba
Manchester City da Newcastle United ba su da wasu 'yan wasan da za su buga Afcon ko kuma Asian Cup.
Saboda haka watakila Pep Guradiola ya yi amfani da rashin Salah domin mayar da kungiyar kan teburin Premier League.
Arsenal za ta ci gaba da wasa ba tare da dan kwallon tawagar Masar ba, Mohamed Elneny da zai buga Afcon, da na Japan Takehiro Tomiyasu wanda zai kara a Asia Cup.
Aston Villa, dan wasa daya za ta yi rashi, shi ne dan kasar Burkina Faso, Bertrand Traore.
Duk da cewar Newcastle ba ta da ƴan wasan da za su je mata Afcon ko kuma Asian Cup, tana fama da 'yan wasa da dama da ke jinya, hakan ya sa take cin karo da koma-baya a wasannin da take yi.