Shin Isra’ila ta ɗauki matakan hana kalaman tunzura kisan kiyashi?

Wani ƙaramin yaro ɗan Falasɗinu a zaune a ƙasa a Khan Younis da ke Gaza a Agustan 2024

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Aƙalla mutum 1.9 ne yaƙin Gaza ya raba da muhallansu-kusan kashi 90 na mutanen zirin - kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.
    • Marubuci, Natalie Merzougui & Maria Rashed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 9

“A ƙona Gaza kawai, babu wani da muke so!" a lokacin da Mataimakin Shugaban Majalisar ya wallafa hakan a shafin X a Nuwamba, kafar ta X ta rufe shafinsa, sannan ta buƙaci ya goge rubutun.

Nissim Vaturi ya yi abin da suka ce, sannan an dawo masa da shafinsa, amma bai bayar da haƙuri ba. Jawabinsa na cikin maganganun da suka tayar da ƙura da manya a Isra'ila suka yi a daidai lokacin da ƙasar ke cigaba da luguden wuta a Gaza, a matsayin martani a kan harin Hamas a Isra'ila a 7 ga Oktoba.

A ranar harin, ya rubuta cewa: "yanzu aiki ɗaya ke gabanmu, mu shafe Zirin Gaza baki ɗaya daga ban-ƙasa."

Wannan rubutun, wanda har yanzu yana nan a shafin X, yana cikin abubuwan da aka gabatar a gaban Kotun Duniya, a lokacin da aka gabatar da tuhumar da ake yi wa Isra'ila, inda Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da kisan kiyashi a yankin Falasɗinawa. Ita dai Isra'ila ta bayyana zargin a matsayin "maras tushe" wanda kuma aka gina "a kan ƙarya da son zuciya."

Daga cikin hukuncin da kotun ta yanke na wucin-gadi. Kotun Duniyar ta ce dole Isra'ila ta hana duk wasu maganganun da suke tunzura kisan kiyashi. Duk da cewa kotun ba ta da damar tilasta aiki da hukuncin, Isra'aila ta amince ta kawo rahoto domin fayyace matakan da ta ɗauka wajen bincike da hukunta waɗanda suka aikata laifin tunzurawa.

Kotun ta tabbatar da cewa ta karɓi rahoton a Fabarairu, amma ba ta bayyana wa duniya ba.

Wasu masana shari'a sun yi amannar cewa Isra'ila ba ta yin abubuwan da suka dace wajen binciken matsalolin. "Isra'ila, wadda take tunzurawa ko kuma take amfani da salon tunzurawa suna da kariya daga hukunci," in ji lauya mai kare haƙƙin ɗan'adam a Isra'ila, Michael Sfard.

Kisan kiyashi na nufin yunƙuri ko niyyar lalata duka, ko kuma wani ɓangare na ƙasa ko ƙabila ko addini. Amma raba tsakanin kalaman tunzurawa da ke jawo rikicin bambancin launin fata - da kuma maganar da za a iya kira ƴancin tofa albarkacin baki - yana da wahalar gaske.

BBC ta duba wasu maganganu da suka fito tun bayan hukuncin Kotun Duniya domin ganin ko an karya hukuncin, sannan ta tambayi masana shari'a domin nazari a kansu. Sannan duk da cewa an yi hukuncin ne kacokan domin Isra'ila, mun yi nazari a kan irin maganar da wasu ƴan Hamas suka yi, inda suke bayyana aniyarsu ta sake maimaita harin ranar 7 ga watan Oktoba.

Itamar Ben-Gvir yana magana a wani taro, inda yake kira da a kafa garuruwan Isra'ila a Zirin Gaza a ranar 28 ga Janairun 2024

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ministan Tsaro Ƙasar Isra'ila Itamar Ben-Gvir yana goyon bayan dokar da ta ba mutanen Gaza damar barin yankin.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam mai goyon bayan Falasɗinawa, wadda ta tattara masana da masu bincike a faɗin duniya, mai bibiyar yaƙin - mai suna Law for Palestine - ta nazarci wasu maganganu da ta yi amannar cewa wasu jami'an gwamnatin Isra'ila sun yi kalaman tunzura jama'a. Ta jera wasu maganganu da Ministan Tsaron ƙasar, Itamar Ben-Gvir ya yi.

Mista Ben-Gvir ya daɗe yana kira da a yi dokar da za ta sa Falasɗinawa su bar Gaza, inda yake cewa akwai buƙatar mutanen Isra'ila su fara zama a Zirin.

Kwana biyu bayan hukuncin Kotun Duniyar a watan Janairu, sai ya fara bayyana buƙatarsa ta a yi dokar da za ta sa Falasɗinawa su fara ficewa daga Gaza, domin mutanen Isra'ila su maye gurbinsu. Ya ce idan ana so a hana yiwuwar sake afkuwar harin Hamas a Isra'ila, "dole mu dawo mu tsare yankin (Gaza)... mu bayar da damar ficewa sannan mu riƙa yanke hukuncin kisa ga ƴan ta'adda," inda ya kawo buƙatar a ba wanda yake so dama ya fice.

"Muna ganin kiran cewa mutanen Gaza su fice daga Gaza a cikin yunƙurin ƙare dangi da ake yi a Gaza," in ji Shugaban Law of Palestine, Ihsan Adel. Ya ce masu yin wannan kiraye-kirayen su ma suna cikin masu tunzura kisan kiyashi, sannan ana aiwatar da kisan kiyashin - zargin da Isra'ila ta ƙaryata.

Sai dai ba kowa ba ne ya amince da fahimtarsa. "Gaskiya ba zan iya kare waɗannan kalaman ba, amma suna ƙara ta'azzara kisan kiyashi," in ji Anne Herzberg, mai ba ƙungiyar NGO Monitor - wadda ke bibiyar harkokin ƙungiyoyin sa-kai na duniya ta fuskan goyon bayan Isra'ila - shawara a kan harkokin shari'a.

Da Mista Ben-Gvir da Mista Vaturi duk sun ƙi amincewa su yi magana da BBC.

Alaƙar da ke tsakanin abubuwan da ƴan siyasa suke faɗa da waɗanda sojojin Isra'ila suke faɗa na cikin abubuwan da Afirka ta Kudu ta gabatar a Kotun Duniya.

A wani faifan bidiyo na 2023, an jiyo wasu dakarun sojojin Rundunar Tsaron Isra'ila, IDF suna cewa, "Ku mamaye, ku kora, sannan ku maye gurbi," sannan sojojin sun yi wasu bidiyoyin bayan hukuncin Kotun Duniyar a watan Janairu, inda suke dariya tare da murnar ragargaza Gaza.

IDF ta bayyana mana cewa ta duba bidiyoyin na intanet, sannan idan ta tabbatar da an yi ba daidai ba, sashen binciken ayyukan soji za su bincika sannan "a wasu bidiyoyin da aka duba, an tabbatar da cewa wasu kalamai ko halayyar da sojojin suka nuna bai dace ba, kuma za a ɗauki mataki."

Wata tankar yaƙi na Isra'ila a Zirin Gaza kusa da bodar Isra'ila da Gaza a Yunin 2024 - za a iya ganin wasu gine-gine da suka ruguje a cikin hoton.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila da suke aiki a zirin Gaza a Yunin 2024

Kullum ana mayar da hankali ne a kan jagoran addinin Isra'ila, Rabbi Eliyahu Mali, wanda ya jawo hankalin duniya bayan maganar da ya yi a Maris a taron wata makarantar masu goyon bayan kafa ƙasar Yahudawa zalla.

Rabbi Mali ne shugaban makarantar ta yeshiva wadda take cikin ƙungiyoyin da suke karɓar tallafin kuɗaɗe daga Ma'aikatar Tsaro ta Isra'ila. Ɗalibanta suna haɗa koyon Attaura da atisayen soji.

Wani faifan bidiyo na maganarsa ɗin da aka yaɗa a kafofin sadarwa, bayan ya kawo wata maganar wani malamin Yahudawa na Ƙarni na 12 a kan jihadi, sai Rabbi Mali ya ce, "(idan haka ne) game da ƙa'idojin da muke da su idan muna yaƙi, a wannan yanayi na Gaza, kamar litattafanmu suka nuna, "ba za a bar ko rai ɗaya ya tsira ba, bayani a fayyace yake - idan ba ku kashe su, za su kashe ku."

A addinin Yahudawa, mitvah na nufin yaƙin kare ƴancin Yahudanci, sannan dole ne a kan kowa ba tare da zaɓi ba.

Da muka tuntuɓi Rabbi Mali, sai ya sa aka aiko da amsa a madadinsa, inda a ciki ya bayyana cewa, "an juya masa maganganunsa ne."

An ce ya bayyana matsayarsu, sannan ya "bayyana a fili cewa a dokar ƙasarsu, "haramun ne cutar da fararen hula da ƙananan yara da tsofaffi."

Mun kalli cikakken bidiyon, inda a wasu wurare a ciki yake sake tunatar da masu sauraron su waɗannan kalaman, har a ƙarshen jawabinsa, da kuma inda ya bayyana a farkon jawabin cewa, "ya kamata ku yi yadda sojoji suka buƙata."

Amma a cikin maganar, ya bayyana wa mutanen Gaza cewa, "ina tunanin akwai bambancin fararen hula mazauna wasu wuraren da fararen hula mazauna Gaza," sannan ya ƙara da wata magana da ba a iya tantancewa, cewa, "kashi 95 zuwa 98 suna da burin ganin bayanmu."

Da wani daga cikin masu sauraron ya tambaya a game da jarirai, sai ya ce, "su ma haka... Attaura ta ce: 'ba za a bar kowane rai ya tsira ba'... idan a yau jariri ne, gobe ya zama yaro, gobe zai iya zama mayaƙi."

A jawabin kuma, rabbi ya kuma bayyana yadda ya faɗa wa ɗansa, wanda ya tafi yaƙi bayan harin na 7 ga watan Oktoba cewa ya "kashe duk wani abu mai motsi." Ya ƙara nanata matsayarsa cewa kwamandan ɗansa ɗin ma ya sake nanata wa yaron nasa, sannan shi kuma ya buƙaci yaron nasa "ya saurari dukkan odojin kwamanda."

Daga baya ya nanata cewa ba ya tunanin sojoji su yi aiki da abin da ke cikin Attaurah. Ya ce idan dokokin Attaurah ɗin suka ci karo da dokokin ƙasar, "su yi amfani da dokokin ƙasar domin dokokin ƙasar ƴan ta'adda suke so a kashe ba fararen hula ba."

Lauya Eitay Mack daga ƙungiyar Tag Meir mai yaƙi da wariya ya ce ya buƙaci ƴansanda su bincika maganganun rabbin bisa zargin tunzura mutane da ta'addanci.

Ya ce yana cigaba da jiran ko a yi binciken da ya buƙata ko ba a yi ba.

Wani mutum yana zaune a kujera wajen tunawa da waɗanda suka mutu a sanadiyar harin na taron kalankuwar ta Nova- a zagaye da wurin akwai tutoci na Isra'ila da na waɗanda aka kashe.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin inda Hamas ta kai hari a 7 ga Oktoba shi ne taron kalankuwar Nova a Isra'ila.

Wani batun da Afika ta Kudu ta gabatar a kotu shi ne "ana fitar da saƙonnin kisan kiyashi a kafafen yaɗa labarai a ƙasar-ba tare an hana ba."

A Fabarairu, a tasha ta 24, ɗan jarida Yaki Adamker ya ce, "ni a tunanina babu laifi idan yunwa ta kashe mutanen Gaza. Ina ruwana da su?"

A Afrilu, wani ɗan jarida a tashar da aka fi kallo a Isra'ila, Channel 12, Yehuda Schlesinger shi ma ya yi irin wannan maganar, inda ya ce, "babu ƴan babu ruwana a Zirin Gaza. Suna ƙaunar Hamas."

BBC ta tuntuɓi dukkan ƴan jaridar domin jin ta bakinsu, amma ba su amince ba. Yehuda Schlesinger shi kuma sai ya amsa ta hanyar nanata harin 7 ga watan Oktoba.

Yahya Sinwar, sanye da kwat buɗaɗɗiya yana ɗaga hannunsa sama.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yahya Sinwar ne ya zama jagoran Hamas bayan an kashe Ismail Haniyeh a Iran a Yuli.

"Hamas ma tana amfani da kalaman tunzurawa, musamman jagoransu," in ji mai bai wa Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila shawara kan shari'a Tal Becker.

A 2021, Yahya Sinwar, wanda a lokacin ne ya zama jagoran Hamas ya ce, "muna goyon bayan shafe Isra'ila a bayan ƙasa ta hanyar amfani da jihadi."

Sannan a kwanan nan, wasu jami'an Hamas sun bayyana suna so su sake aiwatar da hari irin na 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe kimanin mutum 1,200, yawancinsu fararen hula, sannan aka kama mutum 251.

A Nuwamba, wani mamba a sashen siyasar Hamas, Ghazi Hamad ya ce, "dole mu koya wa Isra'ila darasi."

Haka a ƴan tsakankanin wannan lokacin, jagoran Hamas a ƙasashen waje, Khaled Mashaal, ya ce harin na 7 ga watan Oktoba, "buɗe wata hanya ce ta shafe Isra'ila."

Hamas ba ta amsa buƙatar BBC na yin bayani kan waɗannan kalamai ba.

Mutane da dama suna so su ga ƙungiyar - wadda aka ayyana da ta ta'addanci a ƙasashen Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai - ta fuskanci hukunci.

Shugaban Kotun Duniya Joan Donoghue (a tsakiya) da sauran alƙalan kotun sanye da farar riga da baƙar babbar riga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Janairu, Kotun Duniya ta yanke hukuncin cewa dole Isra'ila ta yi duk mai yiwuwa wajen hana kisan kiyashi da kalaman tunzura jama'a.

Amma ba kamar Isra'ila ba, ita Hamas ba za a iya kai ta ƙara Kotun Duniya ba saboda ba ƙasa ba ce. Amma akwai kotun International Criminal Court (ICC) da take da alhakin ɗaukar mataki a kan ɗaiɗaikun mutane.

A Mayu, mai gabatar da ƙararta ya buƙaci a kama jagororin Hamas, Yahya Sinwar da Mohammed Deif da Ismail Haniyeh (An kashe Haniyeh a Iran, sannan Isra'ila ta ce ta kashe Deif) saboda laifukan yaƙi da tauye haƙƙin ɗan'adam. Ya kuma buƙaci a kama Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaron kasar Yoav Gallanta.

A game da abin da Isra'ila ke yi domin hanawa da kuma ladabtar da mutanen da ake zargi da tunzura jama'a, Babban mai shari'a na ƙasar ya tabbatar da cewa wasu kiraye-kirayen a illata fararen hula "za su iya zama laifuka, ciki har da kalaman tunzura jama'a." Kafin shari'ar ta Kotun Duniyar, sun bayyana cewa akwai ƙorafe-ƙorafe da suke bincikawa.

BBC ta tuntuɓi babban mai shari'ar da Kwamishinan Ƴan sanda da Ma'aikatar Shari'a domin jin ta bakinsu. Ma'aikatar Shari'ar ce kawai ta amsa, inda ta ce dole ne su daidaita "haƙƙin furta albarkacin baki... wajen hana kalamam tunzura jama'a." sannan ta ƙara da cewa, "jami'an tsaro suna ƙoƙari wajen bibiya tare da magance kalaman tunzura jama'a."

A daidai lokacin da ake sauraron hukuncin ƙarshe na Kotun Duniyar, mutane suna cigaba da mutuwa - tun daga Oktoba sama da Falasɗinawa 40,000 ne suka mutu a Gaza kamar yadda Ma'aikatar Lafiya wadda take ƙarƙashin kulawar Hamas ta bayyana.

Mene ne kisan kiyashi?

  • Kisan kiyashi: Duk wani abu da aka yi domin shafe duka ko wani sashe na ƙasa ko ƙabila da mabiya addini ko jefa mutane cikin mayuwacin hali da gangan da sauran abubuwan da dokokin duniya suka ayyana a matsayin ta'addanci tun a 1946.
  • Tunzura jama'a: Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kan kisan kiyashi ya bayyana cewa kalaman tunzura jama'a a yi kisan kiyashi laifi ne.
  • Ƙare-dangi: Duk wani mataki daga wata ƙabila ko addini domin shafe wata al'umma ta fararen hula da ƙarfi.

Majiya: Taro kan Kisan Kiyashi na MDD da Hukumar Turai.