Tawagar ƙwararru ta MDD ta buƙaci Isra’ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza

Asalin hoton, Reuters
Tawagar ƙwararru masu kare ƴancin ɗan adam da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, ta yi gargaɗin cewa an kusa a makara wajen hana aikata kisan-kiyashi kan Falasɗinawa a Gaza, biyo bayan luguden-wutar Isra’ila.
Isra’ila ta mayar da martani ga tawagar mai mutum bakwai, inda ta zarge su da maimaita abin da ta kira ''farfagandar Hamas''.
Musayar kalamai tsakanin ɓangarorin biyu na zuwa ne makonni bayan mummunan harin da Hamas ta kai Kudancin Isra’ila.

Asalin hoton, Reuters
Tawagar ƙwararrun ta musamman ta ce yanayin da ake ciki a Gaza ya kai ƙololuwar ƙazancewa, inda ake matuƙar buƙatar abinci da ruwa da magani da kuma sauran muhimman abubuwan gudanar da rayuwa.
Sun ce dole ne Isra’ila da ƙawayenta su gaggauta tsagaita buɗe wuta don kaucewa abin da suka kira shirin Isra’ilar na tarwatsa Zirin-Gaza.
Ƙwararrun sun kuma buƙaci a sako mutanen da masu iƙirarin jihadin ke riƙe dasu a Gazar.
Sai dai kuma Isra’ila ta zargi ƙwararrun na Majalisar Dinkin Duniya da maimaita abin da ta kira farfagandar Hamas, wanda kuma ta ce ba zata lamunta ba.
Isra’ilar ta kuma zargi Hamas da laɓewa a cikin fararen hula, da kuma amfanin dasu wajen bai wa mayaƙanta kariya.
Da yake tsokaci kan bayanin ƙwararrun, wani mai magana da yawun sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce sashin shari’a na Majalisar ne kawai ke iya tabbatar da ko an aikata kisan kiyashi ko kuma akasin hakan.











