Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rufa-rufar da aka yi kan ruftawar ginin cocin T.B Joshua
BBC ta bankaɗo sabbin hujjoji da ke nuna cewa mai katafaren cocin nan na Najeriya, TB Joshua ya ɓoye gawawwaki, kuma ya razana dangin mutanen da lamarin ya ritsa da su, don yin rufa-rufa kan batun rugujewar ginin wanda ya hallaka aƙalla mutum 114 a shekarar 2014.
Rugujewar ginin na ɗaya daga cikin bala'i mafi muni da ya taɓa auka wa wani wurin ibada a Afirka.
Binciken BBC shi ne karon farko da wasu makusantan cocin TB Joshua Synagogue Church of All Nations (Scoan) a Lagos suka gabatar da shaidu na abin da ya janyo faruwar lamarin kusan shekara goma da ta wuce, da kuma yadda aka yi zargin limamin cocin ya kitsa duk rufa-rufar da aka yi.