Kafar Arsenal ɗaya ta yi ban kwana da Champions League

psg

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Paris St Germain da ci 1-0 ranar Talata a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League a Emirates.

PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba.

Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0 a Emirates a cikin watan Oktoba.

Gunners ta ci ƙwallon ta hannun Kai Havertz a minti na 20 da fara wasan, sannan ta kara na biyu ta hannun Bukayo Saka a minti na 15 tsakani.

Karo na shida kenan da suka fafata a babbar gasar zakarun Turai a tarihi, inda Arsenal ta yi nasara biyu da canjaras uku aka doke ta wasa ɗaya.

Wannan shi ne karon farko da PSG ta yi nasara a kan Gunners a gasar ta zakarun Turai da suka haɗu.

Haka kuma wasan farko da aka ci Gunners a gida daga fafatawa 17 a gasar zakarun Turai, wadda ta yi nasara 12 da canjaras biyar, rabon da ta yi rashin nasara a gida tun Maris ɗin 2021 a gasar.

Haka kuma Gunners ta lashe wasa huɗu baya a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyar Faransa, ba tare da an zura mata ƙwallo ba a raga.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasan da aka buga tsakanin Arsenal da PSG a gasar zakarun Turai:

2024/25

Champions League ranar Talata 29 ga watan Afirilu

  • Arsenal 1 - 0 Paris St-Germain

Champions League ranar Talata 1O ga Oktoban 2024

  • Arsenal 2 - 0 Paris St-Germain

2016/2017

Champions League ranar Laraba 23 ga watan Nuwambar 2016

  • Arsenal 2 - 2 Paris St-Germain

Champions League ranar Talata 13 ga watan Satumba 2016

  • Paris St-Germain 1 - 1 Arsenal

1993/1994

Euro Cup Winners Cup ranar Talata 12 ga watan Afirilu 1994

  • Arsenal 1 - 0 Paris St-Germain

Euro Cup Winners Cup ranar Talata 29 ga watan Maris 1994

  • Paris St-Germain 1 - 1 Arsenal

A kakar nan ta bana, PSG ta ci Manchester City 4-2 a karawar cikin rukuni a watan Janairun 2025 a Faransa.

Haka kuma ita ce ta yi waje da Liverpool a zagayen ƴan 16, sannan ta fitar da Aston Villa daga gasar ta Champions League a kwata fainal.

Ranar Laraba 7 ga watan Mayu, Arsenal za ta je Faransa, domin buga wasa na biyu da PSG, inda za a tantance wadda za ta kai wasan karshe a Champions League na bana.

Arsenal da PSG ba wadda ta taɓa lashe Champions League a tarihi.

Tuni PSG ta ɗauki kofin Faransa na Ligue 1 na kakar nan, yayin da Arsenal take ta biyu a Premier League da tazarar maki 15, bayan da Liverpool ta lashe kofin na 20 jimilla.