Martanin gwamnatin Najeriya kan zarge-zargen shugaban Nijar
Gwamnatin Najeriya ta musanta duka zarge-zargen da shugaban mulkin sojin na Nijar, Birgediya Janar Abdurrahamane Tchiani ya yi wa gwamnatin ƙasar na haɗa baki da Faransa domin yi wa ƙasarsa barazanar tsaro.
Ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce Najeriya ba ta taɓa ƙulla wata alaƙar soji da Faransa ko wata ƙasa domin ɗaukar nauyin hare-haren ta'addanci a Jamhuriyar ta Nijar, ko tayar da zaune-tsaye a ƙasar.
Cikin hirarsa da BBC, Mohammed Idris ya ce shugaban Najerya Bola Tinubu a matsayinsa na shugaban Ecowas na gudanar da jagoranci da ya kira 'abin koyi'.
Ya ƙara da cewa Najeriya na martaba daɗaɗɗiyar alaƙarta da Jamhuriyar Nijar.
''Jihohin Najeriya wajen takwas ne suke da iyaka da Nijar ga auratayya da hulɗar kasuwanci, don haka wannan magana da ya yi ba gaskiya ba ne'', in ji ministan
''Kuma Najeriya na iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da ɗorewar danganta mai tarihi tsakaninta da Jamhuriyar Nijar'', in ji Ministan.
Ministan yaɗa labaran na Najeriya ya ce dakarun ƙasar, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen da ke yaƙi a Tafkin Chadi na samun nasara a yaƙin da suke yi da 'yanta'adda a yankin.
''Don haka hikima wani ya yi zargin cewa Najeriya za ta haɗa baki da wata ƙasar waje domin wargaza zaman lafiya da tsaron makwabciyarta'', in ji ministan.



