Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Ghana kai-tsaye
Jam'iyyar NDC mai hamayya na kan gaba a sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Ghana da na 'yan majalisar dokokin ƙasar.
Tuni dai ɗan takarar jam'iyyar NPP mai mulkin ƙasar Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen, tare da taya ɗan takarar jam'iyyar hamayyara, John Dramani Mahama murnar lashe zaɓen.
Wasu daga dama daga cikin manyan ministocin gwamnatin NPP sun faɗi zaɓe a kujerun majalisun dokokin.
'Yantakara 12 ne dai ke fafatawa a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.
Takarar dai ta fi zafi ne tsakanin tsohon shugaban ƙasar John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC mai hamayya da kuma mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia na NPP mai mulki.
Akwai kuma kujerun majalisar dokoki 275 da ake fafatawa a kansu.
Mutum fiye miliyan 18 ne dai suka yi rajistar zaɓe a faɗin ƙasar.