'Abin da ya sa na mayar da $10,000 da na tsinta a jirgin sama'

'Abin da ya sa na mayar da $10,000 da na tsinta a jirgin sama'
An wallafa

Wani matashi ɗan asalin jihar Kano kuma ma'aikaci a Kamfanin Ɗawainiya da Jiragen Sama na Najeriya (NAHCO), yana ci gaba da shan yabo da sa albarka bayan ya tsinci kuɗi dalar Amurka 10,000 a cikin jirgin sama kuma ya kai wa hukumomi.

Auwal Ahmed Ɗankode ya ce ya tsinci kuɗin ne da darajarsu na iya kai wa sama da naira miliyan 15, a lokacin da yake share-share a cikin wani jirgin sama bayan ya sauka a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano.

Ya ce ya mayar da kuɗin da ya tsinta ne saboda nasihar da mahaifinsa yakan yi masa, da kuma horon da kamfaninsu wato NAHCO ke yi wa ma'aikatansa cewa su zama masu gaskiya kuma su riƙe amana.

Auwal Ɗankode ya ce tuni ya samu ƙarin girma a wurin aiki kuma an ba shi lambar karramawa saboda babbar bajinta da ya yi.