Kano Pillars ta samo maki a Sunshine Stars

Kano Pillars

Asalin hoton, Kano Pillars

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sunshine Stars da Kano Pillars sun tshi 1-1 a wasan mako na 25 a gasar Premier ta Najeriya ranar Laraba.

Tun farko sun tashi zagayen farko ba ci sai da suka yi hutu suka koma fafatawa ta biyu aka ci ƙwallayen.

Mai masaukin baki ce ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Chidozie Iwundu daga baya Pillars ta farke ta hannun Eshimutu Gomino.

Da wannan sakamakon Pillars ta koma ta shidan teburi da maki 36, bayan karawar mako na 25.

Ita kuw Sunshine Stars tana ta 17 a kasan teburi da maki 28 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.

Remo Stars ce ta ɗayan teburi da maki 48 mai wasa 24, sai Shooting Stars Sports Club (3SC) ta biyu da maki 41 da Rivers United mai maki 39 ta ukun teburi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga ranar Laraba:

  • El-Kanemi Warriors 0-0 Bendel Insurance
  • Akwa United 1-1 Rivers United
  • Abia Warriors1-0 Rangers International
  • Niger Tornadoes 2-1 Heartland
  • Bayelsa United 2-2 Nasarawa United
  • Ikorodu City 0-1 Plateau United
  • Shooting Stars Sports Club (3SC) 1-2 Lobi Stars

Wasa biyu da za a karasa ranar Alhamis 20 ga watan Fabrairu:

Katsina United FC vs Enyimba FC 4:00 pm Nigeria Premier

Remo Stars FC vs Kwara United FC 5:30 pm Nigeria Premier Football League