Champions League: Ƙungiya uku daga Ingila za ta buga ƴan 16

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiya uku daga Ingila za ta buga zagayen ƴan 16 a Champions League da za a fafata ranar Talata da kuma Laraba.

Liverpool da Arsenal da Aston Villa sun kai zagaye na biyu kai tsaye ba tare da buga wasannin cike gurbi ba a sabon fasalin gasar zakarun Turai ta bana da aka fara.

Ƙungiyar Anfield ce ta yi ta ɗaya a teburin kakar bana da maki 21, bayan cin wasa bakwai da rashin nasara ɗaya daga fafatawa takwas.

Arsenal ta uku ta yi a teburin Champions League da maki 19 daga karawa takwas, wadda ta ci wasa shida da canjaras ɗaya da rashin nasara ɗaya.

Aston Villa kuwa ta kare a mataki na takwas da makinta 16, wadda ta yi nasara biyar da canjars ɗaya da rashin nasara biyu, bayan fafatawa takwas.

Ranar Talata Aston Villa za ta je Belgium, domin fafatawa da Club Brugge, sai Arsenal da za ta je gidan PSV Eindhoven.

Ita kuwa Liverpool sai a ranar Laraba za ta kara a gidan Paris St-Germain a Faransa.

Haka kuma akwai wasa mai zafi da za a buga ranar Talata tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid a Santiago Bernabeu.

Wasannin ranar Talata 4 ga atan Maris

  • Club Brugge da Aston Villa
  • Borussia Dortmund da Lille
  • PSV Eindhoven da Arsenal
  • Real Madrid da Atletico Madrid

Wasannin ranar Laraba 5 ga watan Maris

  • Feyenoord da Inter Milan
  • Bayern Munich da Bayer Leverkusen
  • Benfica da Barcelona
  • Paris St- Germain da Liverpool