Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙudiri uku da zan gabatar idan na ci kujerar majalisa - Amina BB Faruk
Ƙudiri uku da zan gabatar idan na ci kujerar majalisa - Amina BB Faruk
An wallafa
Barista Amina BB Faruk, ita ce 'yar takara mace tilo da ke neman muƙami a matakin tarayya daga faɗin arewa maso yammacin Najeriya.
Lauyar na neman kujerar majalisar wakilai ne daga Mazaɓar Gezawa/Gabasawa da ke Jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai adawa.
Cikin wannan hira ta musamman da BBC Hausa, lauyar ta ce abin takaici ne a ce mace ɗaya ce kacal ke takara daga yankin da ya fi kowanne yawan al'umma a Najeriya.
Ta ƙara da cewa ta tanadi ƙudiri uku da za ta fara gabatarwa a zauren majalisasr da zarar ta yi nasarar lashe zaɓen da za a gudanar a watan Fabarairun 2023.