Europa League: An dage wasan Arsenal da PSV Eindhoven

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An dage wasan Europa League da ya kamata Arsenal ta karbi bakuncin PSV Eindhoven ranar Alhamis a filin wasa na Emirates.

Hakan ya biyo bayan zaman makokin mutuwar Sarauniya Elizabeth II, domin za a samu karancin 'yan sanda da mutanen da za su gabatar da wasu ayyukan a ranar.

UEFA ta ce za ta sanar da ranar da za a buga karawar nan gaba a wasan da tun farko ta tsara ranar Alhamis a Emirates.

BBC ta fahimce cewar za a buga wasan Zakarun Turai tsakanin Chelsea da Red Bull Salzburg ranar Laraba kamar yadda aka tsara.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta kara da cewar ta gamsu cewar za a samar da dukkan jam'an tsaron da za a bukara a filin wasa na Stamford Bridge.

Ana sa ran magoya bayan PSV 3,000 ne za su ziyarci Ingila, domin ganin yadda kungiyarsu za ta fafata da Gunners.