Manyan Premier na rububin matasan Brazil biyu, West Ham ba ta haƙura da Maguire ba

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

West Ham na duba yuwuwar sake neman Harry Maguire, a watan Janairu idan Manchester United ta ci gaba da ƙin sa shi a wasanni sosai. (ESPN)

Ita kuwa Manchester United na sa ido a kan ɗan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 23, kafin zawarcinsa a lokacin bazara. (South London Press)

Manchester City, da Chelsea, da Arsenal da Manchester United na rububin matasan ƴan wasan Palmeiras, ƴan Brazil, Estevao, ɗan gaba mai shekara 16, da Luis Guilherme, ɗan wasan tsakiya mai shekara 17. (90min)

Barcelona na sha'awar ɗan wasan gaba na gefe na Brighton da Japan Kaoru Mitoma, mai shekara 26. (Mundo Deportivo)

A shirye Manchester United take ta bar Anthony Martial ya tafi a watan Janairu. (Football Insider)

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Nottingham Forest Jesse Lingard, 30, wanda rabon da ya taka wa Ingila leda tun 2021, na dab da komawa ƙungiyar Ettifaq ta Saudiyya, amma kuma sai a watan Janairu zai fara wasa saboda dokokin ƙasar a kan ’yan wasan waje. (Sky Sports)

Juventus na sa ran gogayya daga ƙungiyoyi irin su Arsenal, da Manchester City da Brighton a kan ɗan wasan tsakiya na Shakhtar Donetsk da Ukraine Georgiy Sudakov, mai shekara 21. (TEAMtalk)

AC Milan na son ɗauko matashin ɗan bayan Real Betis da Sifaniya Juan Miranda, mai shekara 23 domin nazarin rawar da Theo Hernandez ke takawa saboda a riƙa sa shi a madadinsa a wani lokaci. (Sky Sports)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kociyan ƴan wasan Arsenal ƴan ƙasa da shekara 18 Jack Wilshere, wanda tsohon ɗan wasan tsakiya ne na Ingila na daga cikin masu neman aikin kociyan ƙungiyar Colorado Rapids ta gasar Amurka. (Evening Standard)

Liverpool na sha'awar ɗaukan Bajamushe Max Eberl a matsayin darektan wasanninta. Bayern Munich ma na son Eberl mai shekara 50, bayan da ya ajiye aikin kwanan nan a RB Leipzig. (Bild)

Philippe Clement na son Rangers ta ba shi kwantiragin shekara huɗu idan har tana son ya zama kociyanta amma kuma ƙungiyar Al-Shabab ta Saudiyya ma na sonshi. (Record)

Ajax na son ɗaukar mataimakin kociyan Manchester United Mitchell van der Gaag idan ta kori Maurice Steijn. (Mirror)

Sabbin alƙaluma sun nuna cewa ɗan wasan tsakiya na Real Madrid da Ingila Jude Bellingham, mai shekara 20, tare da abokin wasansa a ƙungiyar, Vinicius Jr sun kasance ƴan wasan da suka fi daraja a gasar La Liga. Kowannensu ya kai fam miliyan 130. (Transfermarkt)

Wasu kafofi da ke da kusanci da Sheikh Jassim sun kafe cewa har yanzu ba abin da ya sauya duk da rahotannin da ke cewa a mako mai zuwa ne ƴan kwamitin gudanarwa na Manchester United za su iya ganawa domin amincewa da tayin da Jim Ratcliffe ya yi na sayen ƙungiyarer. (Mirror)