Masu neman ɗarewa kujerar Tambuwal a Sokoto

Asalin hoton, Media Team
Zaɓen gwamna da za a gudanar a jihar Sokoto da ke arewa mso yammacin Najeriya zai kasance ɗaya daga zaɓuka da za su ɗauki hankali a faɗin, kasancewar zaɓen 'yan majalisun dokoki na tarayya da aka gudanar a jihar ya zo da sammatsi.
Lamarin da ya kai ga hukumar zaɓen ƙasar ta ce dole sai an sake zaɓukan 'yan majalisar dattawan jihar uku da na 'yan majalisar wakilan ƙasar 11 a wasu rumfunan zaɓe.
'Yan takara 17 ne za su fafata a zaɓen gwamna ranar Asabar da za a gudanar a jihar da ake yi wa kirari da birnin Shehu.
Sa'idu Umar - PDP

Asalin hoton, Saidu Umar/Facebook
Saidu Umar Ubandoma tsohon malamin makaranta, ya yi aiki da kamfanin zaba jari na jihar Sokoto, kafin ya yi aiki da bankuna daban-daban na ƙasar, inda har ya riƙe muƙamin mataimakin babban manajan Eco Bank mai lura da shiyyar arewa maso yammacin ƙasar.
Ya kuma riƙe mukamin sakataren gwamnatin jihar Sokoto, inda kuma daga nan ne ya samu zama ɗan takarar muƙamin gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.
Saidu Umar Ubandoma ya riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi a lokacin wa'adin mulkin Tambuwal na farko, kafin a naɗa shi muƙamin sakataren gwamnatin jihar a wa'adin mulkin Tambuwal na biyu.
Ahmed Aliyu Sokoto - APC

Asalin hoton, Ahmed Aliyu Sokoto/Facebook
Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto tsohon ma'aikacin gwamnati kuma ɗan siyasa, wanda ya riƙe muƙamai masu yawa a jihar shi ne ke takarar gwamnan Sokoto a jam'iyyar APC.
Tsohon kwamishina ne a ma'aikatun jin daɗi, walwalar jama'a da al'adu, da ma'aikatar Lafiyar jihar, haka kuma ya riƙe muƙamin sakataren asusun raya ayyukan 'yan sanda, da muƙamin mataimakin gwamnan jihar.
A shekarar 2018 ya sauka daga muƙaminsa na mataimakin gwamnan jihar, bayan da suka fara samun saɓani tsakaninsa da gwamnan jihar Aminu Waziru Tambuwar wanda ya sauka sheƙa zuwa jam'iyyar PDP.
Ahmed Aliyu shi ne ɗan takarar gwamnan jam'iyyyar APC a shekarar 2019, sanna kuma jam'iyyar ta sake zaɓarsa a matsayin ɗan takarar gwaman na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.
Dahiru Umar - NNPP

Asalin hoton, Media team
Sanata Dahiru Umar tsohon sanata ne da ya wakilci Sokoto ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya a baya ya taɓa riƙe muƙamin kwamshina a jihar Sokoto.
Dan takarar na jam'iyyar NNPP, wanda lauya ne kuma tsohon daraktan kamfain ya kasance mamba kwamitin gayaran kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1993 da 1999.
A shekarar 2008 ya zama shugaban ƙungiyar sanatocin arewacin Najeriya, ya kuma shugabanci kwamitin harkokin shari'a na Majalisar dattawan ƙasar.
Umar Aminu Ahmad - LP

Asalin hoton, Media Team
Tsohon ma'aikacin gwamnati wanda ya kai matakin darakta, yana da digiri a fannin sanin halayyar ɗan adam daga jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.
Dan asalin ƙaramar hukumar Sokoto ta Kudu, ya taɓa zama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Sokoto.
Umar Aminu Ahmad shi ne wanda jam'iyyar LP ta tsayar a matsayin ɗan takararta na gwamna a zaɓen da za a gudanar cikin ƙarshen makon nan.
Sauran 'yan takarar da za shiga zaɓen
- Ahmad Ahmad Jao - AA
- Ahmad Babajo Ibrahim - AAC
- Isiyaku Bello - ADC
- Liman Ibrahim Muhammad - ADP
- Ibrahim Muhammed Mansur Gada - APGA
- Abubakar Haruna - APM
- Abba Sidi Ahmed - APP
- Goronyo Ibrahim - BP
- Aliyu Alhaji sulaiman Dandauda - NRM
- Muhammad Sa'idu Gumburawa - PRP
- Umar Abubakar Gada - SDP
- Daniya Usama Sani - YPP
- Mohammed Habibu - ZLP










