Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sanya sunan Mane cikin tawagar Senegal duk da raunin da ya ji
Sunan Sadio Mane ya shiga cikin jerin 'yan wasan da za su bugawa Senegal gasar Kofin Duniya da za a yi a Qatar duk da raunin da ya ji a ranar Talata.
An fitar da dan wasan mai shekara 30 daga fili a minti 45 na farkon wasan da Bayern Munich ta doke Weder Bremen da ci 6-1.
Gwarzuwar gasar Jamus din ta ce Mane ya ji rauni ne a "saman sangalalon kaurinsa na dama" kuma ba zai buga wasan da za ta yi ba da Schalke a ranar Asabar.
Senegal da ke rukunin A za ta fara wasanta da Netherland a ranar 21 ga watan Nuwamba. "Muna sanya idon kan halin da yake ciki, kuma mun tura daya daga cikin likitocinmu ya kasance tare da shi," kamar yadda kocin Senegal Alioy Cisse ya shaida wa taron manema labarai a Dakar babban birnin kasar a ranar Juma'a.
"A ranar Alhamis, Mane yana Munich kafin da yamma ya tafi Australia domin kara yi masa gwaji. Babban abin farin cikin dai shi ne ba za a yi masa tiyata ba.
"Muna so mu duba muga ya lamarin zai kasasnce nan da mako biyu zuwa uku. Ba na so in cire shi daga cikin tawaga."
Tawagar Senegal
Ma su tsaron raga: Seny Dieng (Queens Park Rangers), Alfred Gomis (Rennes), Edouard Mendy (Chelsea).
'Yan baya: Fode Ballo-Toure (AC Milan), Pape Abdou Cisse (Olympiakos), Abdou Diallo (RB Leipzig), Ismail Jakobs (Monaco), Kalidou Koulibaly (Chelsea), Formose Mendy (Amiens), Youssouf Sabaly (Real Betis).
'Yan wasan tsakiya: Pathe Ciss (Rayo Vallecano), Krepin Diatta (Monaco), Idrissa Gana Gueye (Everton), Pape Gueye (Marseille), Cheikhou Kouyate (Nottingham Forest), Mamadou Loum Ndiaye (Reading), Nampalys Mendy (Leicester City), Moustapha Name (Pafos), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur).
'Yan gaba: Boulaye Dia (Salernitana), Famara Diedhiou (Alanyaspor), Bamba Dieng (Marseille), Nicolas Jackson (Villarreal), Sadio Mane (Bayern Munich), Iliman Ndiaye (Sheffield United), Ismaila Sarr (Watford).