Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tunani mara kyau ke sanya mutane shiga bala'i
Alal misali, ashe ka nemi gurbin aiki, sannan aka zabe ka domin zuwa gwaji a zagaye na biyu. Kana alfahari da hakan, sannan ka fara shirin tunkarar sabon kalubale? Ko kuma kana tunanin ba zaka samu aikin ba, da tunanin yadda hakan zai shafi kimar ka? "Idan na kasa samun aikin, na fadi a rayuwa,’’ ka fadawa kan ka.
Ko watakila kana jiran amsar sakon da ka tura wa abokinka. Idan ka kasa samun amsa nan take, za ka fara tunanin dukkanin abubuwan da ka yi ya bata wa mutumin rai – ba tare da la’akari da watakila ayyuka ne suka yi musu yawa ba.
Watakila al’amuran yankuna ne ka fi damuwa da su. Kana daukar tsawon awanni a ko wane dare tunani kan barazanar yakin Nukliya, bullowar wata mummunar annoba mai kisa ko kuma yiwuwar tabarbarewar tattalin arziki.
Barazanar da hakan zai jawo za ta ci gaba da rayawa a cikin zuciyarka.
Cikin dukkan wadannan al’amura ka dauka ka saba da hakan, sannan barazanar za ta saukaka.
Wani abu da tunanin ka zai baka cewa wani abu mara kyau ba zai faru da kai ba, da yayata yiwuwar faruwar lamarin.
Bincike mai yawa ya nuna cewa bala’i na iya haifar da barazana ga lafiyar kwakwalwa, kuma yana iya kara sa mutum jin damuwa tare da yanayin ciwo mai tsanani.
Bala’i na iya faruwa a kowane lokaci a rayuwarmu – amma fargabar da ke tattare da cutar Covid-19, hade da rashin tabbas na siyasa da kuma tattalin arziki, na iya kara tsananta yanayin.
Neman hanyoyin kauce wa tunani maras kyau ya kamata ya karfafa juriyar kowa – kuma watakila babu lokacin da ya fi dacewa don yin koyo.
Kubuta daga tunanin zuciya
Masana halayyar dan adam sun gano cewa bala’i a matsayin babbar barazana ga kwakwalwa ya faro ne daga lokacin haihuwa samun waraka na kwawalwar.
A farkon karni na 20, masana halayyar dan adam – wanda Sigmund Freud da wasu suka kirkira – ya kasance hanyar farko ta magance tabin hankali. Manufar ita ce ta kauce wa fargaba da abubuwan da mutane ke so – galibi abubuwa da suka faru tun lokacin yarinta da jinsi – wadanda ke haifar da matsaloli na tunani.
A cikin tsakiyar karni, masana halayyar ta dan adam kamar Albert Ellis da Aaron Beck, sun fara duba wasu hanyoyi na taimaka wa mutane lokacin da suke cikin damuwa.
Maimakon kokarin bijiro da matsaloli na tunani, sun mayar da hankali kan abubuwan da mutane ke tunani a kai, ta hanyar kaiwa ga wadanda ke tunani mara-kyau ko rashin fahimta da ke janyo wa mutane matsaloli.
Tun da fari, an bayyana bala’i a matsayin wani abu na rashin fahimta – inda wani masani Beck ya yi rubutu a kan rawar da yake takawa na janyo fargaba.
Wani da ke da fargabar shiga jirgin sama, alal misali, zai dauka cewa akwai damuwa cikin dakin matukin jirgin.
Idan basa cikin barazanar shiga bala’i, za su lura cewa ma’aikatan jirgin basu san me yake faruwa ba, amma wanda yake ganin za a iya shiga bala’i zai dauka cewa ma’aikatan cikin jirgin ba sa sa ido yadda ya kamata – idan karar ta ci gaba da faruwa, za su fara tunanin cewa za su mutu.
Bincike ya ci gaba da nuna cewa tunanin kan bala’i, na cikin abubuwa da ke janyo wa mutum matsaloli ko ta rashin lafiya.
Alal misali, a wajen aiki, mai nuna halayen bala’i na iya bata rai kan karamin kuskure.
Keelan ya ce: ‘Za su iya tunani mai ban tsoro kamar ‘za a iya kora ta daga wajen aiki, ba zan iya jure hakan ba,’’ a cewar Keelan.
A wasu lokutan, tsoro da mutum yake ji zai iya kaiwa matakin da ba zai iya aiki ba, Bala’i na iya sa mutum ya gano kansa ga kowane dan canji da aka samu a jikinsa a matsayin alamar ciwon daji.
A wasu lokuta, mutane na iya fara barnar abubuwan jiki wadanda ke tare da damuwa. Alal misali, Idan suna cikin fargaban gabatar da jawabi a wurin taros, suna tunanin cewa bugun zuciyarsu wata alama ce da ke nuna cewa za su kamu da ciwon zuciya.
Sakamakon shi ne karkatar da tunani maras-kyau wanda zai haifar da yanayi na tsoro.
Barnabas Ohst, wani masani kan halayyar dan adam a Freiburg da ke Jamus, kuma marubucin wata takadda da ta yi nazari kan halin dan adam, ya ce jikin mutum na haifar da damuwa da kuma tsoro, wanda hakan zai sa ya fi dacewa a dauka matsayin bala’i.
A cikin tsawon shekaru da suka gabata, bincike ya nuna cewa tunani a kan bala’i zai iya sanya mu cikin barazanar kamuwa da cutukan kwakwalwa – wanda ya hada da rashin lafiya ta kwakwalwa da cuta mai rudarwa har ma da wasu nau'ukan tunani.
Tunanin bala’i na iya kara tsananta zafin jiki. A cikin wannan yanayin, za ayi tunanin cewa wani tsawon lokaci da rashin jin dadi zai kasance – ‘ba zai taba tafiya ba’ – ko dalilinsa.
Alal misali. Za ku iya dauka cewa tsananin ciwon kai na nufin kana dauke da cutar daji na kwakwalwa.
Gwaje-gwaje sun nuna irin wannan tunanin kawai yana kara alamar jin zafi a kwakwalwa, don haka damuwa ya fi tsanani kuma yana daukar tsawon lokaci kafin ya wuce.
Kamar yadda masanin radadin zafi na jami’ar Stanford Beth Darnall da Luana Colloca na jami’ar Maryland, suka rubuta a wata takarda ta baya-bayan nan, wannan mummunan tunani yana ‘kamar daukar gwangwanin man fetur a zuba kan wuta’.
Yanayin damuwa da kan shafi wani
Abubuwa da dama sun bayyana abin da ya sa wasu mutane ke fama da tunani na bala’i fiye da wasu.
Halaye daban-daban na mutane – wadanda ke cikin kwayoyin halitta – za su bayyana wasu bambance-bambancen.
Za mu kuma gano yanayin tunani na ‘yan uwan mu. Idan kana yawan tuna cewa iyayen ka na duba yiwuwar samun mummunar bala’i a kowani biki, za ka iya tunanin hakan ga kowani al’amari na rayuwa.
Bayanin mu zai iya taka rawa. Dalilai na rashin tsaro na nufin mutum zai iya shiga yanayin tunani maras-kyau.
Idan ka fara ganin tunanin ka ya fara raguwa a tsawon shekara Daya ko biyu da suka gabata, hakan ba zai zamanto wani al’amari ba: akwai wasu hujjoji cewa labaran duniya ka iya tsananta bala’in da muke fuskanta.
A wani lokaci, za ka yi tunanin bala’i kan al’amuran – kamar yakin Ukraine da bullowar wani nau’i na annobar korona ko kuma durkushewar tattalin arziki.
A wasu lokutan kuma, hakan kan janyo mutum ya nuna damuwa kan matsaloli da yake fuskanta.
Wani bincike daga jami’ar Sussex da ke Burtaniya, ya tambayi masu yanke shari’a da ke zaman kansu, su bayyana yadda suke ji lokacin kallon labarai daga gidajen talabijin – ko labaran masu dadi ne ko mara dadi ko suna debe-kewa ko kuma basa debewa, masu sanyaya rai ko masu tayar da hankali – sannan da nuna fefe guda 30 da aka zaba ga wadanda aka tambaya su 30.
Kafin su kalli fyafyen da kuma bayan sun kalla, wadanda aka tambayan sun amsa tambayoyi kan manyan damuwowi uku a rayuwarsu, sannan a karshe, sun kuma shiga wata tattaunawa, inda suka tattauna kan Daya daga cikin matsalolinsu.
Kamar yadda ake sa rai, mutanen da suka kalli labarai maras-dadi, su suka fi shiga damuwa kafin kammala kallon fefen kuma sun fi tunani kan bala’i lokacin da suke tattaunawa kan matsalolinsu idan aka kwatanta da wadanda suka kalli fina-finai masu kyau.
Wannan dai bincike ne kan mutane kadan. Sai dai karin bincike ya nuna cewa kallon labarai na yin tasiri kan yanayin mutane wanda hakan kuma zai sauya tunanin mutane.
Ko me yake sa maka damuwa
Ko ma me ya haddasa ma ka damuwa, masana lafiyar kwakwalwa kamar Keelan, ta ce za a iya sanin me yake sa mutane shiga cikin damuwa.
Fadakarwa yana da muhimmanci, don haka mataki na farko ya kamata dakar da tunanin ku da kuma gane lokacin hankalin ku ke tafiya cikin duhu.
Kuna iya lura da cewa kuna jin damuwa game da tattaunawa, misali. Idan tunaninku na gaba shi ne ‘Zan juya shi’, duk da haka, kuna iya tambayar tushen wannan zato.
Wadanne dalilai kuke tunanin za su sa ku gaza? Kuma ta yaya za ku fahimci lamarin bis aga shaidar da ke hannunku?
Idan ka yi kokarin dauka daga wajen mai sanya ido, za ka gane cewa ana iya nuna gazawa, maimakon rashin tabbas – sannan akwai matakai da za ka dauka domin kara baka damar fafatawa yadda ake so.
Ya kamata ku lura game da maganganun da ba su da amfani da kuma wuce gona da iri – yin tunani kamar ‘Na kasa kuma ba zan taba samun aiki ba’’.
A cikin wannan yanayin, kana iya kokarin la’akari da gaskiyar cewa kowa na yin munanan tambayoyi lokaci zuwa lokaci – ba yana nufin sun kasa kwata-kwata ba.
Idan ka gaza, zaka iya koyon wani abu daga wannan gazawar don inganta shirin ka a gaba.
Domin yin la’akari da wani misali, yi tunanin cewa kana da matukar damuwa game da cutar Covid-19, wanda ya mamaye tunanin ku a yanzu.
Duk da yake yana da kyau a gane hadarin kamuwa da cutuka, za ka iya karkarewa da cewa ka kamu da cutar a duk lokacin da kaji dan wani abu cikin makogworon ka, sannan za ka firgita da tunanin yadda za ka iya jurewa idan ka kamu da cutar.
A irin wannan lokaci, za ka karfafa kan ka har sai ka fara nuna alamun cutar – wannan dan abu a cikin makogworon ka na iya zama ba na gaske ba.
Hakanan, kana iya tunatar da kanka cewa allurar rigakafi za ta rage barazanar kamuwa da alamomin cutar masu tsanani, da kuma tunanin yadda za ka warke idan ka kwanta rashin lafiya – ta hanyar kiran abokin ka don yi maka sayayya yayin da kake kwance babu lafiya.