Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe mutane lokacin da aka ƙona ofishin NNPP a Tudun Wada ta jihar Kano
Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta yi zargin cewa an kashe wasu magoya bayanta yayin da aka ƙona ofishin jam'iyyar na Tudun Wada.
Mai magana da yawun NNPP din Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce aƙalla mutum uku ne aka kashe a harin da ƴan APC suka kai ofishin jam'iyyar da yammacin Lahadi.
Ya ce an kuma jikkata wasu mutane 42 da aka harba da bindiga da kuma waɗanda aka sara.
To sai dai shugaban jam'iyyar APC a Kano Abdullahi Abbas ya musanta cewa ƴan jam'iyyarsu ne suka kai harin.
Wani da ya shaida yadda lamarin ya faru ya bayyanawa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da wani ɗan takara na APC ya jagoranci kai harin a daidai lokacin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen yankin.
Ya ce jami'an tsaron da ke wajen sun ringa harbi da bindiga domin tarwatsa maharan.
Mutumin, wanda ya ce daya daga cikin waɗanda suka mutu ɗin ɗan uwansa ne, kuma tuni aka yi jana'izarsa tare da sauran waɗanda suka mutu.
A cewar Sanusi Bature na jam'iyyar NNPP, suna samun rahotannin kai hare-hare ga ƴaƴan jam'iyyarsu a sassan jihar da dama.
Yace a ƙaramar hukumar Ɓagwai ma an jikkata mutanensu 39, a Gwarzo kuma mutum 46 aka jikkata.
A cewar kakakin na jam'iyyar NNPP jami'an gwamnati da ƴan jam'iyyar APC mai mulki ne ke kai hare-haren.
To sai dai a nasa ɓangaren, shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Abbas ya musanta zarge-zargen.
Ya ce abin mamaki ne a zarge su da kai hari a yankunan da suka samu nasara.
A cewarsa, ƴaƴan jam'iyyarsa ba su kaiwa kowa hari ba, hasalima ya zargi jam'iyyar NNPP da kai irin waɗannan hare-hare.
Hukumomin 'yan sanda a jihar Kano sun ce za su gudanar da bincike a kan lamarin domin yi wa BBC karin bayani.