Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da Majalisun Dokokin Najeriya ke sa ran aiwatarwa bayan dogon hutu
A wannan Talatar ake sa ran ‘yan majalisun dokokin Najeriya za su koma bakin aiki, bayan wani dogon hutu da suka yi na wata biyu.
Wannan ne kuma zangon karshe na majalisar, wanda daga shi sai babban zaben da ke tafe a shekara ta 2023.
‘Yan majalisun dai sun tafi hutun ne a fusace, sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar, har wasu na barazanar tsige Shugaba Muhammadu Buhari daga mukaminsa.
Sai dai duk da cewa sun shiga wani lokaci ne na kammala wa’adin majalisar nan da wata tara, ga shi za a fara yakin neman zabe a karshen wannan wata na Satumba, akwai tarin batutuwan da ke dakonsu.
Me ke zaman jiran majalisun?
Daga cikin irin batutuwan da ke zaman jiran majalisun, akwai batun karbar kudurin kasafin kudin 2023 da aka kiyasta zai ci fiye da naira tiriliyan 19 daga Shugaba Muhammadu Buhari.
Don haka sai dai su rairaye na rairayewa, su bar na hankali a cikin kansu.
Sannan yayin tafiyarsu hutu sun bar wata jikakkiya tsakaninsu da bangaren zartarwa sakamakon tabarbarewar tsaro.
Matsalar tsaro ta kai ga ‘yan majalisar da sa wakafi da kuma barazanar tsige shugaban kasar, idan yanayin tsaron bai inganta ba.
Amma Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa, dan majalisar dattawan Najeriyar ya ce tuni sun karbi somin tabi daga wajen Shugaba Muhammadu Buhari kan abubuwan da yake son gabatarwa.
Sannan ya ce a yanzu dai za su soma duba wannan batu.
Kuma akwai shi ma Cif joji na riko da shugaban kasa ke son a tabbatar da shi.
Ya kuma shaida cewa batun tsaro dama sun fusata ne, abin da ya sa suka gargadi shugaban kasar, don haka yanzu za su duba su gani ne ko cigaban ya wadatar ko akwai bukatar sake matsa lamba.
‘Dokokin zaɓe da yajin aikin ASUU’
Dangane da sauran batutuwan da ‘yan majalisar za su karkata gare su da majalisar dattawa da ta wakilai duka maganar daya ce.
Hon Kabiru Alhassan Rurum, ɗan majalisar wakilan ne da shi ma yake shaida wa BBC cewa akwai batun gyaran zaɓe da shi ma za su mayar da hankali a kai.
Sannan akwai matsalolin damina da ambaliyar ruwa da duk za su tattauna a kai.
Dan majalisar ya kuma ce akwai batun yajin aikin malaman jami’oin Najeriyar da ke cikin batutuwan da majalisar wakilan ke Allah-Allah su fara da shi da zarar sun koma bakin aiki.
Hon Rurum ya ce sun gayyaci shugabannin ASUU da ministan ilimi da ɓangaren dalibai domin zaman gaggawa.
Karin haske
‘Yan majalisar dai za su yi zaman hakuri ko maleji ne a wasu zauruka na wucin-gadi da aka tanada musu, saboda kwaskwarimar da ake yi wa ainihin zaurukan nasu.
Kuma watakila wasu daga cikinsu da ba su tsaya ko samun takara ba ne za su juri zaman tun da hankalin masu takara zai karkata ga yakin neman zabe.