Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
World Cup: Ba za a sayar da giya a filayen wasa ba - Fifa
Ba za a sayar da giya ba a filayen wasa takwas da za a gudanar da gasar Kofin Duniya a ƙasar Qatar, a cewar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Fifa.
A da an amince a sayar da giyar ga ‘yan kallo “a wasu lokuna na filayen wasannin”, duk da cewa an haramta sayar da ita a fili a ƙasar da ke bin tsarin addinin Musulunci.
Hakan na nufin mutanen da ke cikin ofisoshi ko wuraren kasuwanci ne kaɗai za su iya samun damar sayen barasar.
A ranar Lahadi za a fara gasar Kofin Duniyar, inda mai masaukin baƙi Qatar za ta take wasa da Ecuador.
Kamfanin Budweiser, ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin gasannin Fifa, yana ƙarƙashin kamfanin AB InBev mai sarrafa giya kuma shi kaɗai ne ke da haƙƙin sayar da ita a gasar Kofin Duniyar.
Bayan tattaunawa tsakanin Fifa da mahukuntan Qatar, an ɗauki matakin tsayar da sayar da giya a dandalin 'yan kallo na Fifa kawai da kuma wuraren da aka yarje wa, amma ban da wuraren wasannin Kofin Duniya," a cewar sanarwar Fifa.
"Fifa da masu masaukin baƙi za su tabbatar da cewa magoya baya sun ji daɗin zuwansu cikin girmamawa."