Al-Ittihad ta nace a kan Salah, Chelsea da Tottenham na rige-rige kan Ansu

An wallafa

Al-Ittihad na shirin biyan fam miliyan 118 don sayen Mohamed Salah, duk da kafewar Liverpool cewa ɗan wasan gaban na ƙasar Masar, mai shekara 31, ba na sayarwa ba ne. (Mail)

Koci Jurgen Klopp zai shiga “ɓacin rai” muddin Liverpool ta karɓi tayin Al-Ittihad ta Saudiyya a kan Salah, yayin da ake rufe cinikin ‘yan wasa ranar Juma'a. (Star)

Tottenham na tattaunawa da Barcelona a kan yarjejeniyar aro ɗan wasan gaba na Sifaniya, Ansu Fati mai shekara 20, tsawon kakar wasanni guda. (Fabrizio Romano)

Ita ma Brighton ta yunƙura don ɗauko Ansu Fati, haka ma Chelsea da Borussia Dortmund sun shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan ƙwallon. (Mundo Deportivo)

Tottenham na duba yiwuwar sayen ɗan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Crystal Palace, Eberechi Eze ɗan shekara 25, bayan kasa cimma yarjejeniya a kan ɗan ƙwallon gaban Nottingham Forest daga Wales Brennan Johnson, mai shekara 22. (Independent)

Manchester United na son ɗauko wani ɗan wasan tsakiya kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan ƙwallo, kuma ɗan ƙwallon Moroco da ke taka leda a Fiorentina Sofyan Amrabat, mai shekara 27, shi ne kan gaba a cikin waɗanda suke haƙo. (Mirror)

Fiorentina ta yi watsi da tayin Manchester United na biyan kusan fam miliyan biyu, don ɗaukar Amrabat a matsayin aro, amma dai tana nazarin wata yarjejeniya da za ta ƙunshi wajabcin sayen ɗan wasan. (Mail)

Manchester United din dai tana kuma tuntuɓar Tottenham don cimma yarjejeniya a kan ɗan wasan tsakiyarta daga ƙasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28. (Sky Sports)

Bayern Munich ma na tattaunawa da Chelsea a ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan baya na Ingila mai shekara 24, Trevoh Chalobah. (Athletic)

Luton Town na shirin ɗaukar ɗan wasan bayan Manchester United na Ingila, Teden Mengi, mai shekara 21. (Mail)

Nottingham Forest tana gab da cimma wata yarjejeniya da Chelsea a kan ɗan wasan gefen Ingila mai shekara 22, Callum Hudson-Odoi. (Guardian)

Sheffield United na jagorantar tseren ɗaukar ɗan ƙwallon tsakiyar Manchester City mai bugawa ƙungiyar Ingila ta ‘yan ƙasa da shekara 21, James McAtee, ɗan shekara 20, a matsayin aro karo na biyu, bayan ya shafe tsawon kakar da ta wuce a filin wasa na Bramall Lane. (Football Insider)

Al-Ittihad sun sanar da Liverpool a kan yiwuwar ɗaukar ɗan ƙwallon bayan Faransa mai shekara 24, Ibrahim Konate. (RMC Sport)

Bayern Munich na shirin ƙaddamar da yunƙurin ɗauko ɗan wasan Fulham mai shekara 28 daga ƙasar Portugal, Joao Palhinha. (Standard)

Arsenal ta amince da sharaɗin zaftare kashi 17.5% a kan farashin fam miliyan 35 da aka yi wa ɗan wasanta na Amurka mai shekara 22, Folarin Balogun ga Monaco. (Mirror)