Ba daɗi buga ƙwallo da kariyar fuska - Mbappe

An wallafa

Kylian Mbappe ya ce ba daɗi buga tamaula da kariyar fuska, bayan da Faransa za ta fuskanci Belgium a karawar zagaye na biyu a Euro 2024 ranar Litinin.

Mai shekara 25 ya ji rauni a karan hanci a wasan farko a cikin rukuni da Faransa ta ci Austria 1-0 a gasar ta cin kofin nahiyar Turai.

Bai buga wasa na biyu ba da suka tashi ba ci da Netherlands, amma ya kara a fafatawa ta uku a cikin rukuni da suka tashi 1-1 da Poland.

A karawar ce Mbappe ya buga da abin kariyar fuska, wanda ya ce bai samu sukuni ba.

Mbappe ya sanar cewar kafin fuskantar Belgium a Dusseldorf ''Yin ƙwallo da abin kariyar fuska ba daɗi.

''Ina ta sauya kariyar fuskar, domin ina cin karo da wani abin da ya kamata a kara ko kuma a cire.

''Gaskiya da wahala, domin yana rage min gani, kuma gumi baya sauka daga goshi, har sai na cire kariyar fuska.

''Amma tunda ina iya cire fuskar kariyar ba wata matsala, kuma bani da wani zaɓi.

''Abin dai ba wani daɗi, amma ina godiya ga kariyar fuskar da ta bani damar buga wasannin.''

An yi wa tawagar Belgium ihu, bayan da ta tashi ba ci da Ukraine, amma Orel Mangala ya ce yana fatan wannan karon magoya baya za su kasance tare da su.

Karawa tsakanin Faransa da Belgium

Faransa ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na hudu da maki biyar. Austria ce ta yi ta daya da maki shida.

Belgium ma ta biyu ta yi a rukuni na biyar da maki hudu iri daya da na Romani, wadda ta ja ragama.

Wannan shi ne karo na 76 da za su fuskanci juna a tsakaninsu a dukkan fafatawa, inda Belgium ta yi nasara 30, Faransa da 26 da canajaras 19.

Belgium ta ci kwallo 162, ita kuwa Faransa ta zura 131 a raga.

Tawagogin biyu sun fuskanci juna a gasar kofin duniya a 2018 a zagayen daf da karshe, inda Faransa ta ci 1-0, wadda daga baya ta lashe kofin.