Gane Mini Hanya: Tare da Sanata Garba Musa Maidoki
Shugaban kwamitin da ke kula da sa ido kan ayyukan Majalisar Dattijai a Najeriya ya yi korafin yadda shugabancin majalisa ta 10 ke nuna son rai wajen tafiyar da harkokin ƙasa, tare da fargabar cewa muddin ba a tashi haikan ba to lamura zasu rincaɓe kuma majalisar za ta kasance tamkar ‘yar amshin shata.
Sanata Garba Musa Maidoki na jam’iyyar PDP daga Kebbi, ya ce duk da cewa ba a sauraransa a kwamitin da yake jagoranta da kuma ba shi damar magana a galibin lokuta a zauren majalisar, ba zai daina ƙoƙari ba wajen ganin abubuwa sun inganta da kuma ci gaba da faɗa wa shugabanni gaskiya wajen kawo saukin matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki da ake fama da su a faɗin ƙasar.
A tattaunawarsu da Umaymah Sani Abdulmumin a kwanakin baya a Landan, ya fara ne da yi mata bayanin yadda ayyukkan majalisar ke gudana a yanzu.