Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matan Ukraine suka koma tuƙa manyan motoci da aikin gadi saboda ƙarancin maza
- Marubuci, Ilona Hromliuk
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Ukraine
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yadda mata ke shiga ayyuka waɗanda a al'ada ake ganin na maza ne na daga cikin hanyoyin da yaƙi ya sauya rayuwar al'umma a Ukraine. Yayin da ake ci gaba da tura samari fagen daga, mata na shiga ayyuka irin na tuƙa manyan motoci da jagorantar kamfanoni da kuma shiga aikin gadi.
Lilia Shulha na tuƙa babbar mota ta ɗaya daga cikin kantuna mafi girma a Ukraine, Silpo.
Ta kasance tana sha'awar aikin tuƙa babbar mota tun tana ƙarama, to amma yaranta ƙanana ne sannan tsohon mijinta ba ya son aikin.
Yanzu ta rabu da mijinta, kuma mahaifiyarta na taya ta rainon yara.
‘Mafarkina’ ya zama gaskiya
A shekaru biyar gabanin Rasha ta ƙaddamar da gagarumin samamen, Lilia ta riƙa aiki a matsayin mai kula da ɗakin ajiye kaya yayin da take kabu-kabu da mota da yamma domin ƙara samun kuɗaɗen shiga.
Ta ce a kodayaushe tana sha'awar tuƙa manyan motoci, kuma ta yi amfani da damad da ta samu wajen koyon tuƙa babbar m,ota.
Lokacin da ta ci jarrabawar koyon tuƙa babbar mota a bara, sai ta gane cewa ashe kakarta ma tana sha'awar aikin.
"Mahaifiyata ta ce min: "Za ki cika burin kakarki, ita ma tana son babbar mota."
Lilia ta ce shiga wurare da kallon dazuka na daga cikin abin da ya fi burge ta game da tuƙa babbar mota.
Ta ce: "Mutane na mamaki idan suka ga na fito daga cikin wannan ƙatuwar motar. Wani lokaci har ɗaukar hotona suke yi."
Lilia ta bayyana cewa tuƙa babbar mota ta zamani ba abu ne mai wahala ba.
"Da zarar ka yi fakin yadda ya kamata, za a sauke kayan. Idan motar ta lalace a kan hanya zan kira a waya a zo a taimaka, haka nan akwai samari da koda yaushe ke da niyyar taimakawa."
A cikin kwanakin nan ta tuƙa motar har zuwa ƙasar Austria mai maƙwaftaka - karo na farko ke nan da ta tuƙa babbar mota zuwa wata ƙasa.
A yanzu, Lilia da takwarar aikinta Natalia, su kaɗai ne mata masu tuƙa babbar mota a kamfanin da suke aiki.
Amma shugaban sashen kula da ma'aikata na rukunin kantin na Silpo, Liubov Ukrainets, ana ƙoƙarin ganin an ɗauki wasu ƙarin mata aiki a fannin na tuƙa manyan motoci ta hanyar ba su horo.
Asali daga tarihi
Bayan kwashe shekara biyu da rabi na samamen da Rasha ke yi a Ukraine, kamfanoni waɗanda ke da mafi yawan ma'aikata maza na fama da yadda za su samu isassun ma'aikata.
Dubban maza ne suka sadaukar da kansu domin fafatawa a fagen daga tun bayan fara yaƙin, kuma tun daga wancan lokaci ake ci gaba da ɗibar dubun dubatar maza a rundunar sojin ƙasar.
A watan Mayu, Ukraine ta fara amfani da wani tsarin ɗaukar aikin soji domin ba ta damar ɗibar sabbin sojoji da yawa.
Ko kafin fara amfani da wannan sabuwar doka, ba ɓoyayyen abu ba ne yadda ake miƙa wa maza takardar ɗaukar su aikin soji a bakin hanya. Saboda haka kamfanoni na cikin haɗarin rasa ayyukansu a kodayaushe.
Kamfanoni masu zaman kansu na da damar hana ɗaukar ma'aikatansu aiki, amma shi ma na kashi 50 ne kawai.
Yawancin mata da ke shiga aikin da asali maza ne suka fi yi tamkar wata dama ce da ta buɗe - suna cimma burukansu yayin da ƙasar ke fama da yaƙi.
Wannan ba shi ne lokaci na farko da ake samun mata na tashi suna maye guraben ayyuka na maza ba.
A ƙasashen Amurka da Birtaniya da wasu ƙasashen da ke yaƙar mulkin ƴan Nazi a Jamus, lokacin yaƙin duniya na biyu, mata sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa tattalin arziƙi.
Zama shugaba
Natalia Skydanovych, wadda ta karanci ilimin haɗa magunguna, a kwanan nan ta tura buƙatar neman aiki a kamfanin Budmix.
Kamfani ne a yammacin Ukraine wanda ke haɗa filastan da ake rufe ciwo.
A maimakon a ba ta muƙamin da ta nema, sai aka ba ta wani muƙami mai girma, a matsayin shugabar ɓangaren harhaɗa abubuwa, domin ta maye gurbin wani namiji wanda ya shiga aikin soja, wata ɗaya da ya gabata.
A baya Natalia ta samu ƙwarewa kan shugabantar mutane ƙalilan, amma a yanzu yawan ma'aikatan da za ta riƙa kula da su ya zamo wani ƙalubale.
"Matasan da ke kan aikin sun fi ni ilimin yadda ake gudanar da aikin, amma duk da haka suna girmama ni, idan aka zo kan wani abu da ban sani ba suna taimaka min, ina jin daɗin hakan. A shirye nake na koyi aikin daki-daki."
‘Warware matsaloli’
Valentyna Tanych wadda ta karanci harkar jinya a yanzu tana aiki a matsayin mai gadi a wani babban kanti cikin kantunan rukunin kantunan ATB.
Shekara ɗaya da ta gabata, tana aiki a kamfanin ne a matsayin akanta.
Ta ce tana sha'awar "aikin gano masu laifi" a lokacin da take ƙarama. Ta ce a lokacin da take aiki a ɓangaren kuɗi ta lura da yadda masu gadi a kantin ke gudanar da ayyukansu.
Lokacin da aka samu gurbin aiki a ɓangaren gadi, sai ta nema cikin hanzari.
Shin mata za su iya cike dukkanin guraben maza?
Ƙasar Ukraine na fuskantar wani gagarumin sauyi a tarihinta, inda aka tarwatsa mutanen ƙasar da dama daga muhallansu, wasu suka watsu a cikin ƙasar wasu kuma zuwa wasu ƙasashen.
Haka nan ma ana samun sauyi a ɓangaren ayyukan yi na ƙasar, kuma an kasa cika guraben ayyuka da dama, musamman a yankunan ƙasar da ke kusa da fagen daga.
Misali, a garin Kryvyin Rih, inda shugaba Zelensky ya fito, wanda ke a kudu maso gabashin Ukraine, wurin da sau da dama Rasha ke yi wa luguden wuta, kamfanin siminti da ke yakin na ta ƙoƙarin ɗaukar mata matuƙa manyan motoci, amma abin na da matuƙar wahala.
Wata jami'a a shafin ɗaukar aiki na Work.ua, Victoria Bilyakova ta ce: "Babu ma isassun mata da za su iya cike gurbin ayyukan da mata suka fi yi sanadiyyar ƙaura da ake yi."
Duk da horo da ake bayarwa da ƙarin girma, babu isassun mata da ke nuna sha'awar yin ayyukan.
Masu lura da harkar ɗaukar aiki a Ukraine sun ce yanzu kamfanoni sun fara komawa ɗaukar tsofaffi da ƴan fansho domin cike irin waɗannan gurabe.