FA na tattaunawa da Tuchel don zama kocin Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Chelsea Thomas Tuchel na tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila kan yadda zai zama kocin tawagar na gaba.
Tun bayan kashin da ta sha a hannun Spain a wasan ƙarshen na Euro 2024 wanda ya ja murabus ɗin Gareth Southgate, Ingila ba ta da tsayayyen koci.
Lee Carsley ne aka tsara yake riƙe da tawagar a matsayin kocin riƙon kwarya, har zuwa ƙarshen watan Nuwamba, yayin da FA ke duba wanda zai fi dacewa da matsayin.
Wasu majiyoyi biyu sun shaida wa BBC cewa tuni aka fara tattaunawa da kocin ɗan kasar Jamus.
An tun tubi kocin Manchester City Pep Guardiola domin yana da sha'awar karɓar aikin na Ingila.
Daga FA har Manchester City babu wanda ya fito bainar jama'a ya yi bayani kan tattaunawar.
A watan Mayu ne Tuchel ya bar Bayern Munich, duk da cewa yana da sauran shekara ɗaya a ƙungiyar, ko da yake hakan ya biyo bayan gaza lashe Bundesliga da ya yi a ƙungiyar karon farko tun kakar 2011-12.
A baya ya rike Mainz da Borussia Dortmund da Paris St-Germain.
Tuchel mai shekara 51 ya riƙa Chelsea tsakanin Janairun 2021 zuwa Satumbar 2022 - Ya lashe Champions Lig da Fifa Club World Cup da Uefa Super Cup gabanin a koreshi.
A watan Yuni, Tuchel ya nuna ƙin amincewarsa da karɓar aikin koyarwar Manchester Unietd - bayan an gano sun tattauna da mai kungiyar Sir Jim Ratcliffe a Faransa.
Idan ya amshi aikin zai zama koci na uku da ya jagoranci Ingila wanda ba ɗan ƙasar ba, bayan Sven-Goran Eriksson da Fabio Capello.










