Ra'ayi Riga: Kan matsalar cin hanci da rashawa 27/12/2024
Matsalar cin hanci da rashawa na daga cikin abbuwan da ke ci wa ƙasashe da dama ciki har da Najeriya, tuwo a ƙwarya.
A baya-bayan rahotonni sun ambato hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, na cewa cin hanci ya yi matuƙar durƙusar da tattalin arzikin Najeriya da ci gaba al'umma.
Haka ma wani rahoto daga hukumar ƙididdiga ta Najeriya tare da haɗin gwiwar ofishin MDD kan yaƙi da miyaƙun ƙwayoyi da manyan laifuka na cewa jami'an gwamnati a Najeriya sun karɓi kuɗin da bai gaza nai biliyan 721 ba a matsayin rashawa a 2023.
Haka a baya-bayan nan hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya ta ƙwace wata unguwa guda mai ɗauke da rukunin gidaje fiye da 750 a Abuja, daga hannun wani tsohon jami'in gwamnatin ƙasar, da ake zargi ya mallaka ta hanyar almundahana.