Abin da ya sa na koma jam’iyyar APC – Shema

Abin da ya sa na koma jam’iyyar APC – Shema
An wallafa

Nijeriya ta faɗa cikin mawuyacin halin, da ke buƙatar duk wani mai kyakkyawar niyya ga ƙasar, ya tallafa wa shugabanni a dukkan matakai da nufin tsamo ta zuwa tudun mun tsira.

Tsohon gwamnan jihar Katsina da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, Barr Ibrahim Shehu Shema ne ya bayyana haka yayin zantawa da BBC a baya-bayan nan.

Ya ce Nijeriya na fama da matsaloli kamar na matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaro musamman a jihohin arewa ciki har da mahaifarsa Katsina, inda rikicin 'yan fashin daji ya raba ɗumbin mutane da garuruwansu.

Shema dai, tsohon gwamnan Katsina ne tsawon shekara takwas a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, kafin a baya-bayan nan, ya yanki katin jam’iyyar APC a mazaɓarsa ta Shema cikin ƙaramar hukumar Dutsin-ma.