Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guardiola zai ci gaba da jan ragamar Man City zuwa 2025
Pep Guardiola ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar Manchester City zuwa karshen kakar 2025.
Mai shekara 51, ya lashe kofi 11 a City, ciki har da Premier League hudu a kaka shida da ya yi a Etihad.
''Tun daga ranar farko na ji cewar da akwai wani abu na musamman a nan, Ba zan kasance a wani wuri da yafi nan ba,'' in ji Guardiola.
''Na kuma ji dadi da zan ci gaba da kasancewa da Manchester City zuwa kaka biyu nan gaba.''
Ya kara da cewar: ''Ba zan iya kwatanta yawan godiyar da nake yi wa kowa a kungiyar ba da yadda da aka yi min, Ina farinciki kuma hankalina a kwance yake, kuma ina da dukkan abin da nake bukata don gudanar da aikin yadda ya dace.
''Na san sabon shafin da za mu bude nan gaba zai kasance mai kayatarwa nan da kaka 10. Ya faru shekara 10 da ta wuce zai kuma ci gaba da faruwa nan da shekara 10, domin kungiyar tana kan turba.
''Ina ji a tare da ni cewar akwai abubuwa da yawa da za mu kara cimma tare, shi ne dalilin da na amince na tsawaita yarjejeniyata, domin mu kara lashe kofuna.
City, wadda ke rike da kofin Premier League tana ta biyu a kan teburin kakar bana da tazarar maki biyar tsakaninta da Arsenal mai jan ragama.
Cikin watan Fabrairu, City za ta kara da RB Leipzig a wasan zagaye na biyu a Champions League.