West Ham ta dauki dan wasan Jamus Fullkrug kan £27m

Niclas Fullkrug

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

West Ham ta amince da sayen dan wasan tawagar Jamus, Niclas Fullkrug daga Borussia Dortmund kan £27m.

Mai shekara 31-ya ci kwallo 15 a wasa 46 a kakar farko da ya buga wa kungiyar da ke taka leda a Bundesliga, wadda ta yi ta biyu a Champions League a bara.

Ya koma Dortmund daga Werder Bremen kan £12.6m kan kakar da aka kammala..

Haka kuma Fullkrug ya ci wa Jamus kwallo biyu a Euro 2024, inda kasar ta kai kwata fainal a gasar da aka kare a cikin watan Yuli, inda Sifaniya ta lashe kofin.

Tun a makon jiya Dortmund ta sanar cewar ta amince Fullkrug ya bar sansanin da take buga wasannin sada zumunta a Switzerland, domin ya je ya gana da wata kungiyar.

West Ham ta shiga kasuwa ne, domin sayen mai cin kwallo, wadda take kuma tattaunawa da dan wasan Aston Villa, dan kasar Colombia Jhon Duran.

Tuni sabon kociya, Julen Lopetegui ya dauki 'yan wasa da suka hada da Max Kilman daga Wolves kan £40m da mai tsaron raga Wes Foderingham daga Sheffield United da dan Brazil, Luis Guilherme kan £25.5 daga Palmeiras.

Haka kuma West Ham tana son sayen Aaron Wan-Bissaka daga Manchester United da dan kwallon Leeds United, Crysencio Summerville.