'Tasirin da NYSC ta yi a rayuwarmu'
'Tasirin da NYSC ta yi a rayuwarmu'
An wallafa
Wasu matasa a Najeriya sun bayyana irin tasirin da tsarin hidimar ƙasa ya yi a rayuwarsu, yayin da aka cika shekara 50 da fara shi.
Gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gawon ta kafa dokar da ta tanadi tsarin ne a ranar 22 ga watan Mayun 1973 don "sake shiryawa, da ginawa da kuma sasanta" 'yan Najeriya bayan yaƙin na basasa.
Akan tura ɗaliban da suka samu shaidar karatu ta digiri ko babbar difiloma (HND) zuwa jihohin da ba nasu na haihuwa ba don yi wa ƙasa hidima. Akasari ana tura mazauna kudanci zuwa arewaci, su ma 'yan arewa haka.
Suhaila Usman da Ibrahim Ballama da Modibbo Dalhatu da Halima sun ce shirin ya koya musu zamantakewa a rayuwarsu.



