Finafinan Hausa biyar da aka nuna a ƙasashen waje

Mamah

Asalin hoton, Abdul Amart/Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Har yanzu masu bibiyar masana'antar Kannywood suna cigaba da bayyana farin cikinsu kan nasarar da aka samu na haska fim ɗin Hausa a ƙasar Saudiyya.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da murnar zaɓen fim ɗin Hausa mai suna Mai martaba da aka yi domin wakiltar Najeriya a babbar gasar karrama finafinai ta duniya wato Oscars wanda za a yi karo na 97 a Amurka.

Haka kuma fim ɗin ya samu shiga gasar karrama finafinai ta Septimius a birnin Amsterdam na ƙasar Netherlands, wanda kuma za a kalla fim ɗin kafin a karrama shi.

Sai dai haska fim ɗin na Hausa da aka yi a Saudiyya ne ya sa masu ruwa da tsaki a masana'antar suka riƙa bayyana farin cikinsu, tare da fatan an ɗora wata sanwa ne a masana'antar, wadda ake fata za ta nuna cikin sauri.

Sai dai a ɗaya ɓangaren kuma, wannan ya sa wasu ke tambayar shin me ya sa ba a samu finafinan Hausa da ake haskawa a ƙasashen duniya, duk da ƙarfin harshe? Sannan me ya sa ake murna?

Wannan ya sa BBC ta tattaro wasu finafinan Hausa guda biyar da aka haska a ƙasashen waje, tare da tattaunawa da masani kan dalilin murnar:

Jalil

Jalil

Asalin hoton, Imdb/website

An shirya fim ɗin Jalil ne a kan ma'aurata, Zahrah (Maryam Booth) da Yusuf (Yakubu Mohammed) da ɗansu Jalil wanda ya kamu da ciwon zuciya kuma ake buƙatar naira miliyan 33 domin yi wa masa tiyata.

Ana tsaka da haka ne kuma aka yi garkuwa da mahaifiyar Yusuf aka buƙaci kuɗin fansa.

A ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2020 ne aka haska fim ɗin a sinimar Plaza Theatre da ke jihar Atlanta na arewacin Amurka.

Kamfanin Noless Studios ne ya ɗauki nauyin shirin, sannan Leslie Dapwatda ya bayar da umarni.

Nanjala

Nanjala

Asalin hoton, Kabiru Musa Jammaje/Facebook

Nanjala fim ɗin Hausa ne da ya tara manyan jaruman fim na kudancin Najeriya irin su Enyinna Nwigwe da Nancy Isime da Segun Arinze da Sola Sabowale, da kuma jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu da Rabiu Rikadawa da sauransu.

Nanjala, wato Nancy ne ta ja fim ɗin, inda ta fito a ƴar jarida. An haska fim ɗin a Turkiyya da Amurka kafin a fara haska shi a Najeriya.

Kabiru Jammaje da Abubakar Bashir Maishadda ne suka shirya, sannan Ali Nuhu ya bayar da umarni.

Mamah

Mamah

Asalin hoton, Abdul Amart/Facebook

Mamah ne fim ɗin da ya ɗauki hankalin mutane lokacin da aka haska shi a ƙasar Saudiyya.

A ranar 9 ga Disamban 2024 ne aka haska fim ɗin a sinimar Red Sea Culture Square da ke ƙasar.

Abdul Amart Maikwashewa da Rahama Sadau suka shirya, sannan Toka Mcbaror ya bayar da umarni.

Mai martaba

Mai martaba

Asalin hoton, Adam A Zango/Facebook

Fim ɗin Mai Martaba shi ne wanda aka zaɓe domin shiga gasar karrama finafinai ta duniya ta Oscars ta 2025.

Fim ɗin ya samu nasarar ne bayan kwamitin tantance finafinan Najeriya sun tantance finafinan Najeriya da suka nuna sha'awar shiga gasar.

An yi fim ɗin ne a jihar Katsina kan tarihin kasuwanci irin na dauri da aka yi tsakanin ƙasashen Afirka.

Prince Daniel ne ya shirya fim ɗin kuma ya bayar da umarni.

An tantance fim ɗin a Amurka, sannan ana tsimayin ranar karrama finafinan, wanda za a yi a ranar 2 ga watan Maris na 2025 a Amurka.

Kakah

Kaka

Asalin hoton, FilmFreeway webiste

Kaka fim ne aka shirya game da garin Duma, wanda yake fama da matsalar garkuwa da mutane da harkokin ƴanbindiga.

Jarumar fim ɗin, Kaka, wadda ta taso a ƙauyen, amma ake abubuwan da ba ta jin daɗi, ta koma rayuwa a birni, domin ta samu ilimi da za ta fitar da ƙauyensu daga ƙangi.

Fim ɗin ya lashe kyautar kwalliya mafi kyau a taron karrama finafinai na TAFF 2024 a Amurka da sauran kyaututtuka.

'Abin da ya sa ake murna'

Habibu Maaruf Abdu

Asalin hoton, Habibu Maaruf Abdu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ganin yadda lamarin ya jefa murna a zukatan masu bibiyar masana'antar da ma finafinan Hausa ne ya sa BBC ta tuntuɓi mai sharhi kan harkokin finafinai, Habibu Maaruf Abdu, inda ya ce abin murna ne, amma akwai sauran aiki a gaba.

A cewarsa, "Ai dole a yi murna, saboda hakan wani muhimmin ci gaba ne ga masana'antar, wanda ke nuna bunƙasa ta fannin ƙirƙira da ingancin finafinai da kuma karɓuwa a duniya. Sannan hakan na iya jawo sabbin masu saka hannun jari, masu tallafawa, da abokan haɗin gwiwa da hulɗoɗin da ka iya haɓaka kuɗaɗen shiga da samar da ayyukan yi a masana'antar."

A game da batun cewa ya kamata a ce finafinan Hausa sun yi fice a sinimomin ƙasashen waje saboda ƙarfin harshen Hausa, Habibu ya ce akwai wasu daliliai da suke jan masana'antar baya.

"Manya daga ciki su ne rashin hanyoyin raba finafinai a sinimomi (distribution network), da kuma ƙarancin masu tallafawa. In ka lura za ka ga Kannywood tun farkonta kusan ta dogara ne a kan kasuwancin bidiyo da CD ba haskawa a sinimomi ba, wanda ake cinikinsu a nan cikin gida da sauran ƙasashen Afrika, har ma da ƙasar Saudiya.

Ya ce yanzu kuma an samu canji komai ya koma tashoshin Talabijin da YouTube, "Sannan akwai ƙarancin masu tallafawa wajen yin tallan finafinan na Hausa a kasashen waje da nemo yadda za'a haskasu a can. Amma Alhamdulillahi, ci gaba ya fara samuwa, tunda finafinan Hausa sun fara karɓuwa a ƙasashen waje."

Sai dai ya ce arewacin Najeriya na da labarai masu inganci da ya kamata a yi finafinai, inda ya ce lallai akwai sakacin furodusoshinmu.

"In ka kula, yawanci furodusoshinmu suna ƙuntace tunaninsu wajen yin finafinai waɗanda iya Hausawa kawai za su burge, yawanci a kan soyayya, zamantakewar aure, rawa da waka da sauransu. Sannan yawancin finafinan ba sa ɗauke da fassarar turanci (subtitle) mai inganci. Su kuma ƴan kudancin Najeriya da suka zo, sai suka dinga ɗaukar muhimman abubuwa da suka shafi arewacin Najeriya, misali matsalar Boko Haram da almajirci, suna finafinai a kai."

A ƙarshe ya ce akwai buƙatar ƴan Kannywood ya kamata su ƙara maida hankali kan yin finafinai masu ma'ana da labarai masu ƙayatarwa na asali ba maimaici ko kwaikwayon indiya ba. Sannan su haɗa kansu waje guda su nemo hanyoyin raba finafinai ba iya Talabijin da YouTube ba.