Barca ta bai wa Real tazarar maki bakwai a La Liga

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta yi nasara a kan Real Mallorca da cin 1-0 a wasan mako na 33 a La Liga da suka fafatawa ranar Talata a Estadi Olímpic.

Barcelona ta ci ƙwallon ta hannun Dani Olmo, suna komawa zagaye na biyu, bayan da ba ci a minti 45 na farkon karawar.

Wannan shi ne wasa na biyu da suka kece raini a tsakaninsu a La Liga, bayan da Barcelona ta je ta ɗura 5-1 a gidan Mallorca ranar 3 ga watan Disambar 2024.

Da wannan sakamakon Barcelona tana da maki 76, bayan wasan mako na 33 da tazarar maki bakwai tsakani da Real Madrid ta biyu mai wasa 32.

Real Madrid za ta je gidan Getafe a wasan mako na 33 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar Laraba 23 ga watan Afirilu.

Daga nan kuma ranar Asabar 26 ga watan Afirilu za a buga wasan karshe a Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid.

Tuni dai Baarcelona ta kai daf da karshe a Champions League, wadda za ta kece raini da Inter Milan gida da waje.

Ita kuwa Real Madrid ta yi ban kwana da gasar zakarun Turai ta bana, sakamakon da Arsenal ta yi waje da ita a zagayen kwata fainal da cin 5-1 gida da waje.

Ƴan wasan Barca da suka fafata da Mallorca a La Liga:

Cubarsí, R. Araujo, I. Martinez, Gavi, Ferran, Pedri, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre, Christensen, Fermín da kuma Pau Víctor.

Sauran sun hada da Lamine Yamal, ⁠Olmo, F. De Jong, Kounde, Eric, Szczęsny, Kochen, H. Fort da kuma Gerard Martín.