Maddison ya ci City ƙwallaye a ranar tunawa da haihuwarsa

Maddison

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

James Maddison ya ci Manchester City ƙwallo biyu a wasan da Tottenham ta yi nasara 4-0 ranar Asabar a Premier League a Etihad.

Kenan City ta yi rashin nasara biyar a jere a dukkan fafatawa, kuma karon farko a tarihi tun bayan 2006.

Pedro Porro ne ya zura na uku sai Brennan Johnson ya ci na hudu, kenan an kawo karshen wasa 52 ba a doke City a Etihad ba.

Rabon da ƙungiyar da Pep Guardiola ta yi rashin nasara a gida tun kafin gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Qatar a 2022.

Wasa mafi muni da aka doke City tun bayan 5-1 da Arsenal ta yi mata a 2003.

Haka kuma karon farko da aka doke City wasa uku a Premier League a jere karkashin Guardiola, wanda ya tsawaita kwantiragin kaka biyu a ƙungiyar.

Tunda Guardiola ya fara horar da tamaula, bai taɓa rashin nasara da cin 4-0 a gida ba a tarihinsa.

City ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier League, amma zai kasance da tazarar maki takwas tsakani da Liverpool ta ɗaya, idan ta ci Southampton ranar Lahadi.

Ita kuwa Tottenham ta yi sama zuwa mataki na shida da tazarar maki huɗu tsakaninta da City.

James Maddison ya yi bikin cikar ranar haihuwarsa ranar Asabar mai shekara 28.