Ko Arsenal za ta doke PSV zagayen ƴan 16 a Champions League?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal za ta ziyarci PSV Eindhoven, domin buga wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League ranar Talata.

Arsenal ta kawo wannan matakin ne kai tsaye, bayan da ta ƙare a mataki na uku a teburin Champions League na bana.

Ita kuwa PSV sai da ta buga wasannin cike gurbi, bayan ta ƙare a mataki na 14 a gasar zakarun Turai ta kakar nan.

Kenan ta kawo wannan matakin bayan fitar da Juventus da cin 2-1 a Italiya, sannan ta yi nasara 3-1 a Netherlands.

Wannan shi ne wasa na 11 da za a kara tsakanin PSV da Arsenal a gasar zakarun Turai, Gunners ta yi nasara huɗu da canjaras huɗu, PSV ta yi nasara biyu.

Rabon da su fuskanci juna tun kakar 2023/24 a Champions League, Arsenal ta fara nasara 4-0 a Emirates ranar Laraba 20 ga watan Satumbar 2023.

A wasa na biyu a Netherlands suka tashi 1-1 ranar Talata 12 ga watan Disambar 2023.

Sun fara haɗuwa a Champions League a kakar 2002/03, inda Gunners ta je ta ci 4-0 ranar Laraba 25 ga watan Satumbar 2002.

Sai suka tashi 0-0 a wasa na biyu a Emirates ranar Talata 12 ga watan Nuwambar 2002.

PSV tana da Champions League da ta ɗauka a 1987–88, yayin da Arsenal ba ta taɓa lashe kofin ba.

Wasanni tsakanin PSV da Arsenal

2023/2024

Champions League Talata 12 ga watan Disambar 2023

  • PSV Eindhoven 1 - 1 Arsenal

Champions League Laraba 20 ga watan Satumbar 2023

  • Arsenal 4 - 0 PSV Eindhoven

2022/2023

Europa League Alhamis 27 ga watan Oktoban 2022

  • PSV Eindhoven 2 - 0 Arsenal

Europa League Alhamis 20 ga watan Oktoban 2022

  • Arsenal 1 - 0 PSV Eindhoven

2006/2007

Champions League Laraba 7 ga watan Maris 2007

  • Arsenal 1 - 1 PSV Eindhoven

Champions League Talata 20 ga watan Fabrairun 2007

  • PSV Eindhoven 1 - 0 Arsenal

2004/2005

Champions League Laraba 24 ga watan Nuwambar 2004

  • PSV Eindhoven 1 - 1 Arsenal

Champions League Talata 14 ga watan Satumbar 2004

  • Arsenal 1 - 0 PSV Eindhoven

2002/2003

Champions League Talata 12 ga watan Satumabar 2002

  • Arsenal 0 - 0 PSV Eindhoven

Champions League Laraba 25 ga watan Satumbar 2002

  • PSV Eindhoven 0 - 4 Arsenal