Hotunan wuraren da Amurka ta kai wa hari a Sokoto da Kwara

..

Asalin hoton, Usman Binji

Bayanan hoto, Ramin da makamin mai linzami da Amurka ta harba kauyen Jabo ya yi, inda kuma ƴan sanda masu kwarewa a harkar abubuwan fashewa ke yin gwaje-gwaje.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2
..

Asalin hoton, Murtala ST

Bayanan hoto, Nan wurin da makamin ya faɗawa ne al'umma garin na Jabo suka zo suna dubawa.
..

Asalin hoton, Usman Binji

Bayanan hoto, Daya daga cikin wuraren da makamin ya shafa kenan a garin Jabo na ƙaramar hukumar Tambuwal da ke jihar Sokoto.
..

Asalin hoton, Usman Binji

Bayanan hoto, Dandazon al'ummar garin Jabo ke zuwa gane wa idanunsu yadda harin ya kasance a daidai lokacin da ƴansandamasu ƙwarewa kan harkokin ababen fashewa ke aikinsu.
..
Bayanan hoto, A garin Offa kuwa harin ya shafi wurare daban-daban ciki har da gidajen otal guda biyu, kuma nan wani daki ne ya faɗa sakamakon ƙarfin makami.
..
Bayanan hoto, Wani matashi ke nan ke nuna raunin da ya samu a kunnensa da gefen wuyansa a lokacin harin na Amurka.
..
Bayanan hoto, Nan kuma wani gida ne da ke kusa da ɗauya daga cikin wuraren da al'amarin ya shafa ne a Offa.
..

Asalin hoton, BBC grab

Bayanan hoto, Hoton da aka ɗauka daga sama na ɗaya daga cikin wuraren da aka kai wa harin na Amurka a garin Offa na jihar Kwara.
..

Asalin hoton, BBC grab

Bayanan hoto, Hoton da aka ɗauka daga sama ya yi ƙasa-ƙasa wajen nuna yadda harin na Amurka ya yi wa gine-gine ɓarna a garin na Offa.