Dembele ya murmure zai fafata da Arsenal

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan gaba na Paris St-Germain Ousmane Dembele yana cikin tawagar da za su fafata da Arsenal a karawa ta biyu zagayen dab da ƙarshe a gasar Zakarun Turai.

PSG ta tabbatar da cewa ɗanwasan ya murmure kuma zai haska a wasan da za ta karɓi baƙuncin Arsenal a Paris.

Dembele ya ɗan samu rauni ne a cinyarsa a fafatawar farko da PSG ta doke Arsenal ci 1-0 a Emirates.

An sauya ɗanwasan bayan hutun rabin lokaci sakamakon raunin da ya ji.

Ɗanwasan mai shekara 27 wanda ya ci wa PSG ƙwallonta a raga, bai buga wa PSG wasan da ta sha kashi ba a Lig 1 hannun Strasbourg, amma ya fito atisaye a ranar Litinin.

"Ya yi atisaye tare da mu a kwanaki biyu," in ji kocin PSG Luis Enrique.

Ya ce ɗanwasan zai haska a wasan ranar Laraba da Arsenal.

Dembele wanda ya koma taka leda PSG daga Barcelona a 2023, shi ne ya fi yawan cin ƙwallaye a raga a PSG inda ya zuwa ƙwallo 33 a dukkanin wasannin da ya buga wa ƙungiyar a kakar bana.