Ra'ayi Riga: Kan haɗakar jam'iyyun siyasa a Najeriya
Ra'ayi Riga: Kan haɗakar jam'iyyun siyasa a Najeriya
An wallafa
Duk da cewa akwai sauran aƙalla shekara biyu kafin babban zaɓen shekarar 2027 a Najeriya, da alama ɓangaren adawa ya fara tuntuɓar juna, domin shirya ƙwace mulki daga hannun jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Tuni dai aka fara ganin taron tattaunawa a lokuta daban-daban tsakanin wasu jiga-jigan ƴan siyasa daga sassan ƙasar.
Na bayan-bayan nan shi ne wanda aka yi a sakatariyar jam'iyyar SDP ta ƙasa, wanda ya samu halarcin wasu ƴan siyasar Arewa da suka haɗa da tsoho gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, da Manjo Hamza Al-Mustapha.
A baya dai an sha yin irin wannan yunkuri, amma hakan na gagara, to ko wannan karon haƙa za ta cimma ruwa? Ya kuke kallon wannan yunƙurin?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirin na wannan mako ya tattauna