Roberts Liam ya nemi afuwata kuma ba na jin da gangan ya dake ni a ka - Mateta

Mateta

Asalin hoton, PA Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Crystal Palace, Jean-Philippe Mateta ya kare mai tsaron ragar Millwall, Liam Roberts, inda ya ce "kiɗimewa ka iya sanya mutum aikata ba daidai ba".

Mateta dai na buƙatar ɗinki 25 a kunnensa na hagu tun bayan da Roberts ya buge shi a kansa a lokacin wasan Palace na gasar FA Cup na ranar 1 ga watan Maris

An fitar da Roberts inda shi kuma ɗan wasan gaban na ƙasar Faransa mai shekaru 27, ya kasance cikin gadon ɗaukar marasa lafiya kafin a hanzarta da shi zuwa asibiti.

Roberts dai mai shekara 30 ya tuntuɓi Mateta domin neman afuwa kafin ƴan soshiyal midiya su fara hantararsa a kafar.

Yayin wata tattaunawa da Sky Sports, Mateta ya ce " Liam ya aike min da saƙo a lokacin da nake asibiti kuma na faɗa masa 'babu komai, ai haka bal ta gada'. Ya nemi afuwa. Ya damu."

An tsawaita haramcin da aka yi wa Roberts zuwa wasanni shida daga uku to amma Mateta bai yarda cewa abin da Robert ɗn ya yi ya yi ne yana sane, inda kuma ya bayyana abin da ƴan soshiyal midiya suke yi da na rashin hankali.

Ba na tunanin ya farka daga barci kawai sai ya yi tunanin "ina son na cire maka kai- JP," in ji Mateta.