Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Feyenoord ta naɗa Bosschaart kocin riƙon ƙwarya
Feyenoord ta naɗa tsohon ɗan wasanta, Pascal Bosschaart a matakin kocin riƙon ƙwarya, kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Talata.
Kenan mai shekara 44, wanda ya maye gurbin Brian Priske, zai ja ragamar ƙungiyar a karawa da AC Milan ranar Laraba a Champions League.
Feyenoord za ta karɓi bakuncin Milan a wasan farko na cike gurbin shiga zagaye na biyu a babbar gasar zakarun Turai ta bana.
Ƙungiyar Netherlands ta kare a mataki na 19 a teburin Champions League, bayan cin wasa huɗu da canjaras ɗaya aka doke ta karawa uku.
Ita kuwa ƙungiyar Italiya ta kammala wasannin cikin rukuni a matsayi na 13, sakamakon da ta lashe wasa biyar da rashin nasara uku.
Ranar Litinin Feyenoord ta raba gari da Priske, saboda rashin samun sakamakon da take bukata, wadda take ta biyar ɗin teburi da tazarar maki 12 tsakani da Ajax mai jan ragama.
Bosschart, ya yi kaka biyu a matsayin ɗan wasan Feyenoord tsakanin 2004-2006, ya kuma horar da matasan ƙungiyar masu shekara kasa da 21.
Ya kuma yi aikin mataimakin koci a ƙungiyar SC Cambuur da kuma FC Dordrecht.