Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd sai ta tanadi £40m kan Mateta, Chelsea na kwaɗayin Hancko
An faɗawa Manchester United cewa sai ta tanadi fam miliyan 40 kan ɗan wasan Faransa, Jean-Philippe Mateta mai shekara 27 da ke Crystal Palace. (Mirror)
Fulham za ta duba yiwuwar gabatar da tayin fam miliyan 40 kan ɗan wasan Amurka mai shekara 27, Antonee Robinson da Liverpool da Manchester United ke hari. (Football Insider)
Roma na iya sayar da Tammy Abraham a lokacin bazara yayinda AC Milan ke nuna ba ta da niyyar saye ɗan wasan da ke zaman aro a sabuwar kaka, sannan ɗan wasan mai shekara 27 ba ya cikin tsarin kaka ta gaba a uwar ƙungiyarsa.(Nicolo Schira)
West Ham da Wolves da Everton na zawarcin Abraham, inda tuni ƙungiyar ta soma tattaunwa da wakilansa. (Calciomercato - in Italian)
Chelsea na bibbiyar ɗan wasan Feyenoord, David Hancko, wanda Tottenham ke cikin ƙungiyoyin da ke harin matashin na Slovakia, mai shekara 27. (Teamtalk)
Everton za ta matsa ƙaimi kan ɗan wasan tsakiya a Denmark, Christian Norgaard mai shekara 30, idan kwantiraginsa ya kare a Brentford a karshen kaka. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya a Juventus da Brazil, Douglas Luiz mai shekara 26, na iya fuskantar musaya da ɗan wasan tsakiya a Newcastle da Italiya, Sandro Tonali mai shekara 24 a wannan kaka. (Calciomercato - in Italian)
Newcastle na son ɗan wasan Sifaniya mai shekara 19 Assane Diao daga Como a lokacin bazara. (Football Insider)
Inter Milan na son daidaitawa kan sabon kwantiragi da Marcus Thuram ganin ɗan wasan na Faransa mai shekara 27, na da damar sauya sheka karkashen yarjejeniyar da ta shata yuro miliyan 85 ga duk mai son sa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Eintracht Frankfurt na bibbiyar ɗan wasan Turkiyya mai shekara 20 Arda Guler da ke Real Madrid. (Sky Sports Germany)
Tsohon kocin Barcelona, Xavi mai shekara 45, ya ce yana son komawa aikin horaswa kuma zai karbi kowanne aiki a wata ƙungiyar La Liga. (France Football, via AS)