Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcola na son zuwa Liverpool, Bayern ba ta son rabuwa da Diaz
Ɗanwasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola, mai shekara 23, ya amince ya koma taka leda a Liverpool, amma babu tabbas kan cinikinsa domin ƙungiyoyin biyu har yanzu ba su sasanta ba kan kuɗinsa. (L'Equipe - in French)
Idan har Barcola ya koma Liverpool zai iya sa PSG ta sha gaban Real Madrid wajen karɓo ɗanwasan Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, daga RB Leipzig. (L'Equipe - in French)
Real Madrid ba ta da niyyar sayar da ɗanwasanta na gaba mai shekara 26 Vinicius Jr na Brazil, wanda yarjejeniyarsa za ta kawo ƙarshe a baɗi, ƙungiyar na da yaƙinin ɗanwasan zai sabunta yarjejeniyarsa. (Sky Sports)
Wasu majiyoyin Newcastle United sun ce babu wata tattaunawa tsakanin ƙungiyar da Arsenal game da Bruno Guimaraes, mai shekara 28. (Northern Echo)
Bayern Munich ba ta da niyyar sayar da ɗanwasan gabanta na Colombia Luis Diaz, duk da rahotanni na alaƙanta shi da Al-Hilal, kuma ɗanwasan ya shaida wa Bayern cewa yana son ci gaba da murza leda. (Sky Sports Germany)
Everton na son fam miliyan 70 kan ɗanwasan Senegal Iliman Ndiaye, mai shekara 26, wanda Manchester United da Al-Hilal ke hamayya. (Mirror)
Manchester United a shirye take ta saki ɗanwasan gaba na Netherlands Joshua Zirkzee yayin a take tattaunawa da Juventus game da ɗanwasan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Nottingham Forest na dab da lale fam miliyan 34 domin sayen ɗanwasan tsakiya na Ivory Coast Ousmane Diomande daga Sporting. (A Bola - in Portuguese)
Ɗanwasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips zai yanke hukunci kan komawa Sheffield United a matsayin aro saboda cire shi daga cikin tawagar City da za ta buga wasannin share fagen kaka. (Mail)