Sancho ya koma Dortmund daga Man United a matsayin aro

.......

Asalin hoton, Fabrizio

Bayanan hoto, Kwallo ta ƙarshe da Jadon Sancho ya ci ita ce a wasan da Uinted ta yi nasara da 2-1 kan Fulham a watan Mayun 2023
An wallafa

Dan wasan Ingila da Manchester United Jadon Sancho ya koma tsohuwar ƙungiyarsa Borussia Dortmund a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar 2023-24.

A watan Yulin 2021 ne, ɗan wasan mai shekara 23 ya koma Old Trafford daga Dortmund kan kuɗi fan miliyan 73.

Tun ranar 26 ga watan Agusta rabon da ɗan wasan ya bugawa United wasa, bayan rikicin da ya faru tsakaninsa da koci Erik ten Hag wanda ya nemi ya riƙa atisayensa shi kaɗai tun watan Satumba.

Babu damar sayan ɗan wasan a sharadin aron da aka ba wa ƙungiyar ta Dortmund.

"Lokacin da na shiga ɗakin sauya kaya a yau, sai na ji kawai na dawo gida," in ji Sancho.

"Na san ƙungiyar ciki da waje, kuna ina da kyakkyawar alaƙa da magoya baya a nan, kuma ban manta da kungiyar ba.

"Na kasa yarda zan sake haɗuwa da abokan kwallona karo na biyu, mu shiga filin wasa mu yi kwallo tare da farin ciki da murna mutaimakawa juna mu ci kwallo mu je gasar Champions."

Tuni Sancho ya isa Jamus inda aka kammala duba lafiyarsa a ranar Laraba, kuma ana sa ran zai ci gaba da atisaye da kungiyar a Marbella.

A bayan ɗan wasan ya shafe shekara hudu a ƙungiyar ta Bundesliga daga 2017, inda ya ci kwallo 50 a wasa 137 da ya buga.

Da ya koma Old Trafford ya yi ta fama da rashin tabbataccen ƙoƙari, inda ya ci kwallo 12 a wasa 82.