Ko Morocco za ta ci Portugal ta kai dab da karshe a Kofin Duniya?

An wallafa

Morocco da Portugal za su kara a wasan daf da na kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar ranar Asabar.

Morocco ta kawo wannan matakin bayan da ta ja ragamar rukuni na shida da maki bakwai mai dauke da Croatia da Belgium da kuma Canada.

Ta kuma doke Sifaniya a bugun fenariti da ci 3-0 bayan da suka tashi ba ci a minti 120 a zagaye na biyu ranar Talata.

Ita kuwa Portugal ta ja ragamar rukuni na takwas da maki shida mai dauke da Uruguay da Koriya ta Kudu da kuma Ghana.

Ranar Talata Portugal ta caskara Switzerland da ci 6-1 a wasan zagaye na biyu, inda Goncalo Ramos, wanda ya maye gurbin Cristiano Ronaldo ya ci uku.

Ya zama na farko da ya ci kwallo uku rigis a wasan farko a Gasar Kofin Duniya, bayan bajintar da Miroslav Klose na Jamus ya yi a 2002.

Wannan shi ne wasa na uku da za a fafata tsakanin tawagogin biyu a Gasar Kofin Duniya, inda Morooco ta ci 3-1 a 1986, Porugal ta yi nasara da ci 1-0 a 2018 duk a karawar cikin rukuni.

Kwallo 12 Portugal ta zura a cikin raga a Qatar kuma 'yan wasa takwas ne suka ci kwallayen a tawagar.

Kwallo daya ne ya shiga ragar Morooco a wasa hudu a Gasar Kofin Duniya a Qatar, wanda ta yi 2-1 da Canada a cikin rukuni.

Wannan shi ne karon farko da Morocco ta kai daf da na kusa da karshe a tarihi, za kuma ta zama ta farko daga Afirka da za ta buga daf da karshe a Kofin duniya, idan ta ci Portugal ranar Asabar.