Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Southgate ya caccaki na'urar VAR
Kocin Ingila, Gareth Southgate, ya soki tsarin mataimakin alkalin wasa na bidiyo (VAR) saboda mummunan tasirin da yake yi ga magoya bayan wasan.
Jami’an na VAR sun kasa sauya hukuncin lokacin da aka yi kuskuren soke kwallon da ɗan wasan Liverpool Luis Diaz ya zura a wasan da Tottenham ta yi nasara a kansu da ci 2-1 a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Tuni kocin Reds Jurgen Klopp ya yi kira da a sake buga wasan.
Southgate ya bayyana dalilin da ya sa ba ya son VAR a ranar da ya bayyana tawagarsa ta Ingila a wasannin da za ta yi da Australia da Italiya.
Duk da haka ya yarda da cewa kwallon kafa ba zai koma zamanin da ba a amfani da fasaha wurin yanke hukunci ba.
Da yake karin haske game da yadda yake ji game da VAR, Southgate ya kara da cewa: "Abin da zan ce shi ne a wancan lokacin kowa ya kan je mashaya ya yi korafi game da alkalin wasa kuma har yanzu suna zuwa mashaya suna korafi kan alkalin wasa, har yanzu babu abin da ya canza''.